Hukumar NAPTIP ta ceto mutane 17,443 da akai safararsu tun kafuwarta. Fatima Abdullahi Bintulhuda Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (...
Hukumar NAPTIP ta ceto mutane 17,443 da akai safararsu tun kafuwarta.
Fatima Abdullahi Bintulhuda
Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP), ta kubutar da mutane akalla 17,443 da suka tsira daga safarar mutane tun kafuwarta a shekarar 2003.
Kwamandan shiyyar Benin da ta kunshi jihohin Edo, Delta da Bayelsa, Mista Nduka Nwanwenne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron wayar da kan jama’a a Ologbo, karamar hukumar Ikpoba-Okha ta Edo.
Nwannwenne ya kuma ce hukumar ta samu akalla laifuka da basu gaza 502 tun bayan kafa ta.
Ya ce shirin wayar da kan jama’ar, anyi shi ne don neman hadin kan cibiyoyin gargajiya wajen yakar matsalar safarar mutane.
Kwamandan shiyyar ya ce za a gudanar da irin wannan shirin na wayar da kan jama’a a wasu al’ummomi biyu na jihar.
Ya ce an shirya shirin ne tare da hadin gwiwar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bekwara/Ogbudu/Obanliku a Kuros Riba, Mista Legor Idagbo.
Ya shaida wa jama’a cewa a ko da yaushe masu fataucin suna fakewa ne da taimakon wadanda abin ya shafa cewa zasu samu ingantattun damammaki a kasashen waje.
Nwanwenne ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su, galibi ana kai su kasashen waje ne ta haramtacciyar hanya da kuma hadari, galibi suna cikin tsananin matsi da É—imuwa. Wasu ma sun mutu kafin su isa inda suke," in ji shi.
Ya koka da yadda wasu iyaye sukan tilasta wa ‘ya’yansu yin irin wannan balaguron ba tare da sanin illar da ke tattare da hakan ba.
“Dalilin wannan shawarwarin shi ne don a wayar da kan jama’a kan illar safarar mutane domin yawancin wadanda abin ya shafa sukan ce ba su taba sanin matsalolin nuna ba ba kafin su fara niyyar wannan tafiya.''
“Suna zuwa wurin mutane su sa musu tunanin cewa a Turai zasu dinga samun kudi kaman tsintar su ake a kasa, ba haka bane, suna yi ne kawai don amfani da su a matsayin bayi, karuwai ko masu safarar kwayoyi.' Don haka ne muka zo gare ku, sarakunanmu da iyayenmu, domin mu sanar da ku cewa dole ne mu hada kai domin dakile wannan matsalar. Mu yada labarai game da fataucin mutane a cikin al'ummominmu," in ji shi.
Kwamandan shiyyar ya ci gaba da bayyana cewa jihohi 20 ciki har da jihar Edo sun kafa rundunar yaki da safarar mutane ba bisa ka’ida ba, ya kuma bukaci sauran jihohin da su yi hakan.
Da yake mayar da martani a madadin sarakunan, Aigbedion na Masarautar Benin, Cif Godspower Irorere, ya ce shawarar ta bude ido ga galibin su.
Ya bukaci hukumar da ta gudanar da shirin a wayar da kan al’umma a ilahirin fadin jihar.
Source Jarida Radio
No comments