Shari'ar Abduljabbar: Malamin yayi wa masu karar sa gyara akan tuhumar da suke masa a gaban kotu. Dan Bala Malam Abduljabbar Kabara...
Shari'ar Abduljabbar: Malamin yayi wa masu karar sa gyara akan tuhumar da suke masa a gaban kotu.
Dan Bala
Malam Abduljabbar Kabara ya yiwa wadanda suke karar sa gyararraki a Tuhumar da aka gabatar gaban kotu kansa. Ya yi hakan ne yayin da yake kariya akan abinda ke kunshe cikin tuhuma ta 3 da aka gabatarwa kotu.
''A karshen karshe da masu gabatar da kara suke cewa wannan magana ta korewa ma'aiki SAWA wannan kazanta da nayi ya saba da sashen da suka dogara dashi, ina tabbatar musu ka'ida ta shari'ar Muslunci da suka ambata karkashin maganar bata yadda da taba ran musulmi ba sai idan ƙa'idoji na taba ransa sun cika cif''
''Dan haka a cajin ya zama dole su ambaci nau'in ɓatancin da ake zubar da jini akan sa duba da hadisi na 4037 cikin Bukhari da Mai lamba ta 1801 cikin Muslim'' Inji Malam Abduljabbar
Malamin ya bayyana cewa abinda yake wajibi bayan tantance wanne irin nau'in batanci ne, shine manufar wanda aka jingina wa fadar ɓatancin. Ya kafa hujja da hadisi na 2744 cikin sahihu Muslim.
''Sannan ya wajaba kafin su kai ga rubuta wannan sashe, su tabbatar cewa mai yin wannan furucin ba bisa ga dole yayi ba, bisa dadin rai yayi, sharaÉ—in na cikin Alqur'ani a sura ta 94 aya ta 106. Ya kamata suyi la'akari da cewa Musulunci ya ginu akan adalci magami, ba wai ga Musulmi ba kadai, harda kafiri. Dan haka a cikin Alqur'ani suratul Isra'i aya ta 15 Allah yace (Bama kasancewa masu azaba har sai mun aiko manzo)"
''Koda a cikin karatuttuka na bana cewa wanda yaji kuskure yazo ya gyara mun, balle ina fada, wannan aya tana wajabta cewa sai an bi wannna rukuni, an yanke hanzarin ka. Sai wadannan sun hadu, anan ne za a tuhume ni a taho kotu, wanda ba daya daga wadannan da akai. Wannan shine suka ta akan kunshin tuhuma ta 3'' inji Malam Abduljabbar.
A zaman yau, malamin yayi kariya ne akan kunshin tuhuma ta 3 wacca ke dauke da cewa ya yi amfani da lafazin Fyade da kuma kwace ya nasabtawa hadisin Bukhari da Muslim. A cikin kariyar tashi ya ambato manyan Limaman Musulunci da yace suma duka sun kawo dalilai na haramta wannan aure da aka ruwaito Annabi yayi da Nana Safiyya sun kuma tabbatar ba ayi haka ba kaman yadda Shima ya ke korewa. Daga cikin Limaman, ya ambaci Limamin Mazahabin malikiyya Imam Malik, Abu Hanifa, Laisu bn Sa'ad Almisry, Ibn Shibruma, Muhammad binil Hassan Asshaibaniy, Zufar bnl Huzair, Ibnl MurabiÉ—i, AbuÉ—É—ayib AÉ—É—abariy, da kuma Jabir bn Zaid.
A zama na gaba Malamin zai É—ora ne da kariya akan kunshin tuhuma ta 4 dake jerin tuhume-tuhume da aka gabatar a gaban kotu kansa.
Source Jarida Radio
No comments