Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

An Sace Kudin Sadaki Ana Kasa Da Daurin Aure

An Sace Kudin Sadaki Ana Kasa Da Daurin Aure Wani abun kamar a fim amma kuma ace zahiri ne tabbas wannan labarin akwai nishadantarwa sosai...

An Sace Kudin Sadaki Ana Kasa Da Daurin Aure

Wani abun kamar a fim amma kuma ace zahiri ne tabbas wannan labarin akwai nishadantarwa sosai a cikin amma kuma wanda ya wallafa labarin dan zaria ne ko dai barkwancin da ke tsakanin kanawa da bazazzage ne sunka tashi. Kamar yadda wani shafi mai suna Daily News Hausa sunka ruwaito a facebook suna cewa.

“A jiya laraba ne 16/03/2022 akaje daura aure daga garin Igabi na jihar Kaduna, zuwa Kano kamar yadda rahotonnu ke tabbatar mana da hakan, “Inda aka nemi sadaki sama ko kasa ba’a Ganshiba.

Sakamakon hakan yasa aka bata lokaci ba’a daura auren ba ana ta kallon kallo a tsakanin juna, Amma daga bisani aka gani a cikin babban rigan daya daga cikin waliyan amarya, inda yace shi bai ma San yadda akayi kudin suka zo jikinshi ba anan dai aka kori waliyin zuwa waje. Inda aka Kira kanin shi da yazama cikon waliyyan amaryan.

Wannan lamari ya farune a kano a wata unguwa da ake kira da kurna.”

No comments