X DA DUMI DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Cire Tallafin Kudin Wutan Lantarki Da gaske ne, mun cire tallafin wutar lantarki. Duk wata 6 zamu...
X
DA DUMI DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Cire Tallafin Kudin Wutan Lantarki
Da gaske ne, mun cire tallafin wutar lantarki. Duk wata 6 zamu ƙara kuɗin wuta - NERC
Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya NERC ta tabbatar da labarin cewa gwamnatin tarayya ta cire tallafin wutar lantarki kuma an kara kudin wuta.
Shugaban hukumar, Mr Sanusi Garba, ya bayyanawa manema labarai a Abuja cewa an yi hakan ne bisa tsarin da akayi na kara kudin wuta bayan kowani wata shida.
Garba yace hakkin hukumomin rarraba wuta ne su sanar da kwastamominsu cewa an kara kudin wuta.
Wannan na faruwa ne lokacin da wutar kasar ta lalace kusan kwanaki biyu a jere.
Garba yace wutar ta samu matsala ne saboda fasa bututun mai da ake yi da kuma lalacewar layi 330KV dake Ughelli.
Yan Najeriya da dama suna kokawa, kasancewar matsalar rashin hasken wutar lantarki na daga cikin manyan matsalolin da suka dade suna ci musu tuwo a kwarya.
Masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arziki na ganin cewa, muddin ba a samu tsayayyar wutar lantarki ba, toh kuwa tamkar an kama hanyar zama koma baya ne wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki da kuma rashin aikin yi.
No comments