Duk Ayyukan Zunuban Da Nake Yi, Ba Na Yin Shirka, Cewar Jarumar Fina-finan Kannywood, Umma Shehu Fitacciyar tauraruwar finafina-finan Kann...
Duk Ayyukan Zunuban Da Nake Yi, Ba Na Yin Shirka, Cewar Jarumar Fina-finan Kannywood, Umma Shehu
Fitacciyar tauraruwar finafina-finan Kannywood ta ce ta bar masu zaginta da Allah domin kuwa shi ne zai saka mata.
Ta bayyana haka ne a hira da ta yi da majiyar Blueink News Hausa, BBC Hausa domin yin raddi ga masu zaginta bisa zargin tana aikata ba daidai ba.
Ta ce a matsayinta na Musulma, tana yi wa Allah laifi kuma ta san zai gafarta mata amma duk da irin laifukan da take yi masa "ba na yin shirka."
Tauraruwar ta ce ya kamata masu ganin ta aikata ba daidai ba su rika jan hankalinta ba kawai su rika zaginta ba.
A cewarta masu zaginta na kallo za ta shiga aljannah ta bar su suna dakon zunuban da suka dauka saboda zaginta.
No comments