Gidan Badamasi Episode 13 F I N A L E A Cikin Wannan Shiri Shine Na Karshe A Cikin Wanan Season Na Hidan Badamasi Episode 13 Inda Zakuga ...
Gidan Badamasi Episode 13
F I N A L E
A Cikin
Wannan Shiri Shine Na Karshe A Cikin Wanan Season Na Hidan Badamasi Episode 13 Inda Zakuga Cewa Badamasi Ya Mutu Inda Zakuga Yadda Aka Zo Gidan Akayi Masa Wanka Inda Mutane zsukazo Gidan Dan Kwambo Yana Tambayarsu Akan Cewa Ko Babansu Badamasi Yana Binsu Kudi Ne Inda Aka Samu Wani Mutum Yace Shi Fa Ya Na Bin Badamasi Kudi Har Biliyan 2 Biyu Inda Dan Kwambo Ya Hada Yaran Yana znuna Musu Cewa Su Basu Yarda Fa Wannan Hukuncin Ba Kuma Basu Yadda Yana Binsu Kudi Ba
Ga Kadan daga cikin shirin
Yau da karfe 8:00 na dare
A tashar @AREWA24Channel
Maimaici karfe 1:00 na dare
Ko gobe Juma’a 9:00 na safe
GIDAN BADAMASI EPISODE 13 AKWAI KURAH
Akwai tirka-tirka da kumbiya-kumbiya kwarai da gaske a fim din Gidan Badamasi inda a halin yanzu dai duk masu kallo suna da masaniyar cewa Badamasi Uban 'Ya'ya ye ya riga mu gidan gaskiya.A wannan lokacine aka hangi babban dan wannan hamshakin attariji wanda kowa yasan kankamo ne shi shine ma yasa yaran nasa suke ta yin dukkanin makircin da zasu iya domin ganin sun sami damar cin kudin nan amma hakan yaki samuwa.
Dankwambo shine babban dansa inda bayan an yi wa Badamasi wankan gawa ne kamar yadda aka saba a al'adar musulunci sai an tambayi mutane cewa ko akwai masu bin sa bashi kafin a binne shi. Sai Dankwambo yayi tambaya cewa ko akwai wanda yake bin mahaifin su bashi anan ne aka sami wani mutumi ya ce shi yana bin sa kudi har Naira Bilyan Biyu.
Koda jin haka sai 'yayan Mamacin suka yi tsalle suka tuma suna cewa ai basu san wannan zance ba, ma'ana basu yarda a taba musu ko sisin kwabo ba.
Don haka sai ku biyo mu sau da kafa domin ganin yadda zata kare domin munga da alama *Alh Badamasi bai mutu ba domin Taska ya fahimci haka yayin da yaga gawa tana motsi.
