Kungiyar daliban Najeriya ta kasa, NANS ta ba gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU wa’adi zuwa ranar 28 ga ...
Kungiyar daliban Najeriya ta kasa, NANS ta ba gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU wa’adi zuwa ranar 28 ga watan Maris don su shirya da junayensu su kuma dakatar da yajin aiki.
NANS ta bayar da wannan sanarwar ne ta wata takarda wacce ta saki a ranar Laraba ta shugaban ta, Sunday Ashefon, The Punch ta ruwaito.
Ashefon ya ce idan hakan bai tabbata ba daliban Najeriya zasu bi titina suna zanga-zanga. Kamar yadda takardar ta zo:
“Muna shawartar gwamnatin tarayya da ASUU akan su yi iyakar kokarin su wurin daidaitawa daga yanzu zuwa ranar 28 ga watan Maris na 2022 ko kuma mu dauki namu matakin.
“Muna fatan daga yanzu zuwa ranar 28 ga watan Maris shugabannin ASUU da gwamnati zasu duba illar da wannan lamarin yake da shi ga kasar mu baki daya don su yi gaggawar kawo mafita.
“Ya kamata majalisar tarayya ta yi iyakar kokarin ta wurin ganin ta kawo karshen yajin aikin nan a cikin wannan datsin.
Tunda sun hana amfani da dokar da ta hana ma’aikatan gwamnati fitar da yaran su karatu zuwa kasashen ketare, don haka ya kamata su gyara mana makarantun mu don hakan aikin su ne.
No comments