Lokacin Auren Ta Yayi Amma Rashin Lafiyar Dake Damunta ke Hana Auren Daga:- Yushau Garba Shanga Wannan Baiwar Allah Da Kuke Gani Yan U...
Lokacin Auren Ta Yayi Amma Rashin Lafiyar Dake Damunta ke Hana Auren
Daga:- Yushau Garba Shanga
Wannan Baiwar Allah Da Kuke Gani Yan Uwanta Sunzo Ofishin Kungiyar Nan Mai Taimakon Marayu Da Marasa Lafiya Mai Suna Patient And Destitute Welfare Organization PADWO Dake Garin Argungu Don Neman Taimakon Jama'ar Musulmi Karkashin Wannan Kungiya.
Malama Hadiza Allah Ya Jarrabeta Da Wani Rashin Lafiya Da Idan Ya Taso Mata Takanyi Fama Da Wadannan Abubuwa Kamar Haka.
1- Kan Ta Zai Kabe Yayi Kunburi
2- Zata Daina Ji
3- Zata Daina Gani
4- Numfashi Ya Dauke Wata Rana Sai Ta Suma
Saboda Wani Abu Ke Tsirowa Ga Makoshin ta Ya Rufe Kussuwar Hanncin ta Da Makogwaron Ta Ya Hana Mata Numfashi
Iyayen Ta Duk Sun Rasu Yanzu Tana Hannun Yayan ta Wanda Yake Shi Kuma Talakka Ne.
No comments