Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

SALON DA MALAM DAURAWA YA DAUKA, IRIN SALON ALLAH NE DAGA DR ASSALAFY

  SALON DA MALAM DAURAWA YA DAUKA, IRIN SALON ALLAH NE DAGA Datti Assalafiy Da bana son in fadi komai Amma sai naga abin ya fara komawa wani...

 SALON DA MALAM DAURAWA YA DAUKA, IRIN SALON ALLAH NE

DAGA Datti Assalafiy


Da bana son in fadi komai Amma sai naga abin ya fara komawa wani abin daban, musamman a wajen 'yan nanaye da 'yan boko akida mata.


Ni, a waje na, duk mutanen da suke ta kumfan baki akan kalaman Malam Aminu Daurawa da yayi akan "Gaban Mata" wanda ya jawo cece kuce daga jiya zuwa yau dinnan, ni kawai na dauke su a matsayin daya daga cikin mutum ukun nan ne.

(ii) Jahili

(ii) Munafiki

(iii) Mazinaci

In baka cikin wadannan mutanen banga abinda zai ma zafin da har kana fade-fade ba a social media


ME MALAM YA FADA?


Cewa yayi: "Idan kace mace ce dadin duniya to menene a jikin macen? mafi muni a jikin mace shine gabanta, nan take fitsari take fitar da jini, to menene abin burgewa? shiyasa aka boyeshi ai, inda shi mata suke nuna wa gudu za'ayi, sai fuska itace mafi kyawu a jikin mace, to da kyawun fuskar zata jaka zuwa ga mafi munin abinda ke jikinta, bashi da kyan gani, ta nan take fitsari, kashi da jini da fitar yaro, to me zai ja hankalinka a duniya da har zai rabaka da Allah?" Domin cikakken bayanin da Malam Aminu Daurawa yayi zaka iya shiga wannan link din  https://youtu.be/oqr2YXAIZlE

SHARHI NA

#Scientifically (Anatomically), gaban Mata ya kasu kashi tara ne (9), sune kamar haka:

(1) Sheep Woman 

(2) Cat Woman

(3) Buffalo Woman 

(4) Bear Woman 

(5) Wolf Woman

(6) Antelope Woman

(7) Deer Woman

(8) Fox Woman

(9) Dancing Woman

Duk jinsin mata na mutum, ko a ina kike,  Africa ne ko Turai, Asia ne kike ko a Middle East, Fara ce ko Baka, Doguwa ce ke ko Guntuwa, "Private Part" dinki yana cikin daya daga cikin wadannan category guda taran. (In kinga dama zaki iya dubawa a gida domin confirmation 😎)


Bisa ga maganar Malam, kamar yadda zaku gani a cikin hoto da ke a kasa, wanda aka dauka a littafin "Anatomy and Physiology". dukannin su taran babu wacca take da "kyau" a dai kyawun gani kam

Medically, duk wanda yake Gynecologist, Nurse, Midwife, ko Surgeon, koma Generally fuk mai aikin kiwon lafiya da yake alada da V.E ko karbar haihuwa zai tabbatar ma da wanga zance


Kamar yadda Malam yake fadi, kowace mace "Kyawun Fuskar ta" ne yake rufe mata munin Gaban ta, kafin aje ga launin fata ko kyawun jiki da dai sauran su.


Note: kar fa mu manta da cewa bawai ana maganar tozarci ko kaskanta mata bane ko kuma akan wajen bai da amfani bane ba. A'A! aasali ma, kusan kaso 80% na maza buga-bugan su da rayuwar su gabada ya ya kare ne akan samun wannan wuri mai albarka, Directly or indirectly. 🙈🙈

Sannan, kaso 90% na mata, iya rayuwar su, takamar su, neman su, samun su, rayuwar su gaba daya yana ta allaka ne da maintaining na wurin Directly or indirectly.🤷🏾‍♂️


Sannan kuma ba wai iya na matan bane kadai mai munin, na mazan ma tafiyar duk guda daya ce, haka Allah (SWT) Ya tsara kayan Sa.😎


MAKASUDIN MAGANAR MALAM DAURAWA:

Asalin bayanin shine a kwadaitar da mutane ga gudun duniya da ababen da suke sawa mutum sha'awar duniyar, karshe har yaje yana sabon Allah saboda su, acikin su harda mata, wannan shine makasudin maganar Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Allah (T) da kanSa Ya ce ya kawata wa mutane kwadayi da sha'awar Mata  da ababen more rayuwa, Allah Ya ce ba iya su ba kenan jin dadin duniyar?

Indai ka fahimci maganar Malam ta wata siga mummuna, to wannan kuma dkwakwalwar kace take da matsala, amma ba kalaman Malam ba


Daurawa Malami ne masanin Al-Qur'ani da Hadisin Manzon Allah (SAW), don haka duk salo ko Philosophy na maganar sa zai zamo daga salo ne irin na Allah ko Annabawan Allah

YA SALON ALLAH TAKE?

gaba daya a cikin Qur'ani, duk inda Allah Zai yiwa bayinSa gargadi da "gudun duniya" ko "gujewa saba masa" da kalaman kaskanci ko kazanta yake amfani.


Misali:

Idan Allah Zay yi gargadi akan "Girman kai" sai Ya tunawa 'dan-Adam fa cewa "duka-duka shi 'dan-Adam ba komai bane, mutumin da aka halicce ci daga 'Turbaya' "طين" ko  "ترب" ina ya ga abin takama, harda yin dagawa?"

A wani gurin kuma Allah yace da 'dan-adam  "mun halicce shi daga digon maniyyi, ' نطفۃ'da gudan jini 'علقۃ '" dan haka wanda aka samo shi daga wadannan, ina shi ina jiji da kai harda yin sabon Allah?


Idan kuma gargadin ya shafi "Zina" ne, kai tsaye da kalmar "Kazanta" " فحشاء" Allah yake amfani dashi.

Jama'a.. da 'Turbaya' da 'Maniyyi' da 'Jini' acikin su duk akwai abinda ba kazanta bane ba?


Akwai mai yin wanka ne ya shiga suturar sa mai kyau, sannan kuma yana ji yana gani zai je ya zauna a tabo? Meyasa ba zayyi ba? wannan kam mun san amsar.. 

Akwai mai yadda ya fita daga gida ga shiga gari da maniyyi manne a kayan sa? Ai har kunya kunya sai ta kama shi idan ya ankara, a misalance kenan


Amma mai yasa Allah (SWT) da kanSa ya ke buga misali da gargadi gare mu, da wadannan ababen tare da ma kama sunan su kai tsaye?  Saboda Ya gwada ma kai ba kowa bane, Dan haka ka kiyaye kanka ka dauki darasin, ka gujewa munanan dabi'u.


SALON DA  DAURAWA YA DAUKA, IRIN SALON ALLAH NE.

Ibrahim Ismail Alnafad


Allah Ka fahimtar damu, Ka sa mu fi karfin son zuciyar mu, Ka nuna mana gaskiya Ka bamu ikon binta Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

No comments