Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Ki Gaggauta Tuba Tun Kafin Allah Ya Nuna Miki Sakamakon Ki A Gidan Dubiya

 Ki Gaggauta Tuba Tun Kafin Allah Ya Nuna Miki Sakamakon Ki A Gidan Dubiya  Daga Muhammad Kwairi Waziri Wata fitsararriya yarinya 'yar n...

 Ki Gaggauta Tuba Tun Kafin Allah Ya Nuna Miki Sakamakon Ki A Gidan Dubiya 


Daga Muhammad Kwairi Waziri

Wata fitsararriya yarinya 'yar nanaye taci mutunci babban Malami addinin Musulunci "Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa" akan wata magana daya furta cewa, babu abu mafi kazanta ajikin mace kaman farjinta.

Da wannan kalmar ne  wannar yarinyar Nafisa Ishak tayi amfani wajen cin mutunci da zagin malamai masu daraja da kima aduniya wadda sunfi irinki ninkin ba ninkin.

Nafisa Ishak ki tattara hankalin ki waje guda domin ki duba kalmar da kika furtawa malami masu daraja wadda hakan zai iya shafar al'umma baki daya, balle ke kanki, hakika da kin san kuskuren zagin malamai masu daraja kamar su "Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa" da baza ki aikata hakan ba.

Hakika harkar film ke bai zamo miki alheri ba, domin ya fitar dake daga hayyacin ki, domin duk wani musulmi ko wadda yake cikin hayyacin sa bazai furta haka ba.

Nafisa Ishak Inada tambayoyi da nake so ki amasa min gasu kamar haka 👇 👇👇

Mutum nawa ne suka shiryu ta dalilin ki?

Mutum nawane suka musulunta dalilin ki??

Marayu nawa kika maida su masu gata??

Dalibai Nawa kika karantar??

Mutane nawa kika yi Sanadiyar lalata musu tarbiya ??

Kefa baki da wani amfani ga al'umma ko kwara daya kai wani baita ba jin sunan kiba saida ki aikata wannan tsiyar.

Banta ba tsammanin rashin kunyar ki ya kai haka ba saida kika farta wannan kalaman amma ki san cewa, wlh Allah bazai barki ba kijira Sakamakon ki anan kusa tun a gidan duniya ko ki gaggauta tuba ga Allah.

Ina so ki karanta wannan maganar da fiyeyyen halitta ya fada  zaki san waye malami 👇👇👇👇

Manzon Allah tsira da aminci Allah S.A.W yace, "mutuwar malami mutuwar dukkan halittune hatta abinda baya motsi kamar bishiya, saboda mahinmancin malamine yasa ANNABI S.A.W yafada haka".

Malamai Sune Magadan Annabwa Inji Manzon Allah SWA.

Manzon Allah S.A.W yace, "lokaci na zuwa gaba al'umma ta zasu raina Malaman kwarai sannan su watsar dasu wato suna musu kallon banza, to wlh sai Allah ya jarabce su day masifa guda uku".

Gasu kamar ka haka 👇👇👇

1) zasu ringa yin sana'a Amma babu albarka acikin ta, Ma'ana zaka ringa samun kudi a cikin sana'ar ka amma kullum burin ka yana karuwa, yana sana'a amma kullum sai kukan babu yake fadi saboda an dauke albarkan cikin ta.

2) Allah S.W.A zai jarabce al'umma da shugabanni azzalumai Marassa tausayin talakawan su idan har suka kasan ce suna zagin malamai magadan annabawa.

3) zaga mutane suna mutuwa acikin addinin Musulunci amma basa cikawa da imani, tsabar talauci ya sanya suna sabawa ubangiji.

Daga karshe kuma kira ga sauran 'yan Uwa na maza da mata damu kaura cewa zagin malamai kai ba malamai kadai ba koma waye saboda addini Musulunci bai karantar damu haka ba.

Rubutawa ✍️✍️✍️✍️ Muhammad Kwairi Waziri

No comments