SHIRIN LULU DA ANDALU. Film ne da ba'a taba yin irinshi a Kannywood ba. Labari ne da ya faru a gaske. Rubutawa Shariff Aminu Ahlan Fas...
SHIRIN LULU DA ANDALU.
Film ne da ba'a taba yin irinshi a Kannywood ba. Labari ne da ya faru a gaske.
Rubutawa Shariff Aminu Ahlan Fassarawa Yaya Muhammad.
Part-1
Masana'antar shirya fina finan Hausa Kannywood ta zarce tunanin masu tani, musamman wanda yasan yadda masana'antar ta faro sama da shekaru talatin baya zuwa yanzu. Nayi imanin wani zai gaskata abinda nake fada cewar an samu cigaba kwarai da gaske wanda hakan yasa duniya tasan da zaman masana'antar a matsayin masana'antar dake bun kasa cikin hanzari sakamakon irin nagartattun fina finan da ake samarwa, duk kuwa da kalu balan kudi da take fuskanta biyo bayan karancin samun tallafi ko zuba jari daga bangaran gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin film na Duniya.
Zuwa yanzu masanaantar shirya fina finan Hausa ta dauki wata sabuwar turba ta cigaba, wanda nan gaba kadan duniya zata kara gamsuwa da aiyukan Kannywood wanda hakan zaisa masana'antar ta fara karbar manyan lambobin yabo a mataki na Duniya, sakamakon fara daukar wani ingantacce kuma nagartaccen sabon shirin film mai dogon zango maisuna "Lulu da Andalu" wanda duk kanin abinda labarin ya kunsa abu ne da ya faru a zahiri.
MANSA MUSA wani shaharerren mai dukiya ne dan kasar MALI wanda tarihi ya tabbatar da cewa ya taba zama mutumin da babu wanda ya kaishi tarin dukiya a fadin duniya, yayi mulkinsa a matsayin MANSA na MALI tsakanin shekara ta 1312 sannan kuma ya rasu a shekara ta 1337.
Sai kuma kwatsam a wannan zamanin namu na shekara 2022 aka sami wani bawan Allah wanda burinsa shine ya gano inda dukiyar MANSA MUSA take domin ya mallaketa, sai dai kafin gano inda dukiyar MANSA MUSA take dole sai an taso da wasu hatsabiban Aljanu guda biyu wato LULU da ANDALU daga wani dogon barcinsu na shekaru sama da 700 da suka gabata suna shekar kayansu.
Haka kuma shirin film da zai nuna yadda dangantaka da mu'amular rayuwa ke gudana tsakanin bil'adama da 'Jinnu" ke kasan cewa ta yadda mutum da aljanu zasuyi aiki tare wajan gano maboyar wani sirri na tarin dukiyar MANSA, inda bil'adama da jinnu za suyi amfani da tsafi wajan gudanar da aikinsu. Ko ta yaya hakan zai yuwu?? Wannan na daga cikin tarin tambayoyin da zuwa yanzu
No comments