Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

VIDEO: Rurrun Gume Hasana Muhammad Da Bashir Mai Shadda Yayi Kafin A Daura Aure Yajaa…

  VIDEO: Rurrun Gume Hasana Muhammad Da Bashir Mai Shadda Yayi Kafin A Daura Aure Yajaa… bayyanar wani sabon video a wajen daukar hotunan au...


 VIDEO: Rurrun Gume Hasana Muhammad Da Bashir Mai Shadda Yayi Kafin A Daura Aure Yajaa…

bayyanar wani sabon video a wajen daukar hotunan auren Bashir Mai Shadda Da hassana muhammad ya jawo masa cece kuce a kafafen sada zumunta musamman tiktok da YouTube

 Duk da kasancewar duniya ta sani cewar an saka masu ranar aure Kuma ana gab da yin auren amma mutane dayawa sunata ala wadai da abinda bashir Mai Shadda yayi domin ba musulunci bane kuma ba al adar hausawa bace

sai dai kuma wasu daga cikin mutane sam sam basa daukar wannan a matsayin wani tafka kuskure ko abinda bai dace ba saka makon suna ganin hakan soyayyah ce kawai ta kawo hakan

wasu kuma gani suke idan wasu sunyi baace komi ba ae Bashir Mai Shadda da hassana muhammad su shahararrune don haka dole yazamana sunayin taka tsantsan wajen duk abubuwan da zasuyi domin a zauna lafiya


ana dakyau mutane mu gane cewa aure fa ba wasa bane musamman ma a mahangar addinin Musulunci da al'adar Hausawa ma bai kamata ba cewa ango ya dinga rungumar wadda zai aura alhali ba'a daura aure ba wannan haramun ne ga-da-ga.

Auren Bashir Maishadda ya bar baya da kura domin kuwa a free wedding (bikin kafin aure) anga wani bidiyo na ta yawo a kafafen sada zumunta musamman manhajojin youtube da tik tok inda Maishadda ya yi ra rungumar amaryar sa Hassana inda hakan yabar baya da kura, domin kuwa mutane da malamai na ta tofa albarkacin bakin su tare da nuna rashin jin dadin su duba da cewa tabbas Maishadda yayi wa addinin Musulunci da kuma al'adar Hausawa karan tsaye.

Anan muna kira ga dukan Musulmi da su din ga kare mutuncin addini da kuma al'ada a duk wani lamari da zasu gudanar na rayuwa. Su guji are aren al'adu domin inganta tasu.

Hausawa sunce sai bango ya tsage kadangare yake samun wajen shiga. Sannan kuma da dangari akan ci gari. Don haka bai kamata ba Hausawa musamman ma celebrities su dinga yin wani abu da ba daidai ba saboda su ake kallo.


No comments