Wani Attajiri Ya Cikawa Budurwarsa Alƙawari Kamar Yanda Ya Ɗaukar Mata Kafin Ta Mutu. Daga Aliyu A Tsiga Attajirin nan ɗan Najeriya ya bin...
Wani Attajiri Ya Cikawa Budurwarsa Alƙawari Kamar Yanda Ya Ɗaukar Mata Kafin Ta Mutu.
Daga Aliyu A Tsiga
Attajirin nan ɗan Najeriya ya binne budurwarsa a cikin wata mota ƙirar Hummer Jeep domin cika alƙawarin da ya ɗaukar mata lokacin da take da rai.
Hamshaƙi attajirin nan ɗan Najeriya mai suna Cif Ade Azikie ya binne budurwar tasa da wata mota ƙirar Hummer SUV mai tsada maimakon akwatin da aka saba yi a lokacin da ta rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a makon jiya.
A cewar wani shaidar gani da ido, attajirin ya yi alƙawarin bai wa budurwar soyayyar a lokacin da take rashin lafiya ta yadda zai ƙarfafa mata gwiwa ta samu lafiya.
Abin takaici kafin wani lokaci budurwar ta ce ga garin ku nan. Lokacin da ta mutu, ya yanke shawarar cika alƙawarin da ya yi mata ta hanyar tabbatar da cewa ta shiga ƙarƙashin ƙasa a cikin motar ƙirar homa jeep.
An yi bikin binne gawar ne a wata ƙaramar al'umma inda wasu mazauna garin ba za su iya cin abinci murabba'i 3 ba a rana. Hamshaƙin attajirin ya damu cewa wasu mutane na iya sace motar don haka ya ba da umarnin a sanya mata siminti da yawa. Ya kuma ɗauki masu gadi har mutum 6 aiki don su sa ido a kan wannan inda zai dinga biyan su duk wata.
No comments