Jama'a sun cafke dan kai sako a jihar Legas yayin da aka kama shi da jinjiri a cikin akwatin kai sako. Daily Trust ta ruwaito cewa, l...
Jama'a sun cafke dan kai sako a jihar Legas yayin da aka kama shi da jinjiri a cikin akwatin kai sako.
Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Sangotedo da ke jihar Legas yayin da fusatattuna jama'a suka far wa matukin babur din kai sakon.
Wani bidiyon lamarin da ya faru an wallafa a Twitter inda aka bayyana ana nadar dan sakon yayin da ake jan shi a kasa har zuwa ofishin 'yan sanda.
Daya daga cikin mutanen da ke wurin an ji yana cewa: "Wannan shi ne jinjirin da aka sace."
Har a halin yanzu 'yan sanda ba su yi magana kan aukuwar lamarin da ya janyo cece-kuce duba da yawaitar miyagun laifuka a jihar.
A yayin rubuta wannan rahoton, ba a gano yadda aka yi jaririn ya shiga akwatin ba.
Sanannen abu ne yadda yankin Sangotedo da ya hada da Ajah, Abijo da Lekki suka zama fitattun yankunan a Legas da aka fi samun masu laifi
No comments