DUNIYAR BUDURWAN WAWA Jama'a ku saurari sakon wannan yarinya 'yar Tiktok, tace wai an kai karanta gidansu don tana yin Tiktok. ...
DUNIYAR BUDURWAN WAWA
Jama'a ku saurari sakon wannan yarinya 'yar Tiktok, tace wai an kai karanta gidansu don tana yin Tiktok.
Yarinyar tace ita bata jin magana, ko maganar iyayenta bata ji balle na wasu, a kyaleta kawai taci duniyarta da tsinke, ko Malamai bata son suyi mata nasiha, don ba zata saurara ba, duniya kawai take so.
Wannan itace misalin irin matan da duniya ta aure su, kuma duniya zata kaita ta baro ba da jimawa ba.
Watakila a yanzu tana takama nonuwanta a tsaye suke, tana da tudun mazaunai, gayu da sauran lalattu fajirai suna kashe mata kudi tana walawa a duniya, shiyasa take izgili.
To ku bata shekaru 10 nan gaba, tabbas nonuwan zasu zube, tudun mazaunan da take jan hankali dasu zasu shafe, launin fatarta zai canza kala ya yankwane, hakora zasu fara faduwa, watakila a lokacin ko kare ba zai shinshi ta ba balle mutum
Ko ba mutuwa dole watarana a tsufa, idan an biyewa duniya ba'a yi aure aka haifi yara ba har tsufa yazo, zasu dawo suna kashi da fitsari a kwance babu 'ya'ya balle jikoki da zasu kula da su, kudin da suka tara a neman duniya su kare, kowa ya gudu ya barsu su zama abin kyama a cikin al'ummah.
Rayuwar irin wannan matan abin tausayi ne, duk Musulmin da yayi watsi da Allah ya kama duniya dole a tausaya masa, kuma wanzuwar irin wadannan mata 'yan duniya cikin al'umma su kulla kawance da Salihan mata hatsarii ne babba, domin zasu gorbata su.
X
DAGA Datti Assalafiy
No comments