Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

ALAQA SEASON 2 EPISODE 5

 ALAQA SEASON 2 EPISODE 5 Fim din Alaqa ya kasance fim mai dogon zango irin sa na farko a Masana'antar Kannywood dake Arewacin Nijer...

 ALAQA SEASON 2 EPISODE 5

Fim din Alaqa ya kasance fim mai dogon zango irin sa na farko a Masana'antar Kannywood dake Arewacin Nijeriya domin kuwa ya samu ingantaccen labari kuma mai rikitarwa da rudarwa sannan kuma ga nishadantarwa domin kuwa salon aikin sa irin na manyan masana'antun fina finai na duniya musamman ma Hollywood da kuma fim din Korea ta yadda baza ka iya gane tabbacin abin da zai faru a gaba ba.

A Episode na 4 a Season 2 akwai abubawa masu ban mamaki da suka faru tsakanin Hisham (Shamsu Dan'iya) da Ciska (Auwal Isa West) domin kuwa kowa yasan sun kasance abokan adawar juna inda a karshe ma har kasaiyya suka yi a wajen siyen fili inda Hisham din ya sami nasara a kan Ciska, amma wai sai gashi wai a karshe Ciska ya taimakawa Hisham ya rage masa hanya sakamakon matsala da motar su ta samu.

Hisham ya yi godiya a gare shi Ciska amma Ciska ya nuna masa cewa ya manta da komai an riga an zama daya ya kuma nemi da su zama abokai inda wasu masu kallo ke ganin akwai lauje cikin nadi domin kuwa ta farat daya bazai yiwu ace an zama abokai haka ba.

A daya bangaren Aunty Hauwa (Fatima Makamashi) da Hajiya Fatima (Hadizan Saima) da Ummi (Maryam Yahya) da Hajiya ta Bawa da Halisa (Maimuna Abubakar Momy Gombe) da Fatima Abubakar (Fati Yola) suma fa a nasu bangaren akwai bakala duk akan auren nameer (Ramadan Booth).

ALAQA SEASON 2 EPISODE 5

Kawai dai ku biyo mu a Episode na 5 domin ganin yadda zata kaya hatta tsakanin Kamal (Danta Bashir) da abokin karawar sa.

                         

YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS).📖✍🏽✍🏽✍🏽 

No comments