Ali Madagwal Ya Bawa Sarkin Waka Hakuri Inda Yace -Tunda Mun fada Masu Gaskiya sunki ji Allah ya Shiryesu idan masu shiryuwane Sarki ...
Ali Madagwal Ya Bawa Sarkin Waka Hakuri Inda Yace -Tunda Mun fada Masu Gaskiya sunki ji Allah ya Shiryesu idan masu shiryuwane Sarki
Kamar dai yadda kuka sani a kwanaki biyun nan ne aka samu rashin jituwa Tsakanin jaruma Nafisat Abdullahi da kuma Mawaki Naziru Sarkin Waka inda jarumar ta wallafaa shafinta na twitter inda take cewa bai kamata mutane suna haihuwar yaran da bazasu iya kulawa dasu ba.
Hakan yasa sarkin waka ya maida Martani cewa ai idan kana neman yaran da aka haifa aka kasa kulawa dasu to taho Masana'antar fim bayan dai faruwar wannan Iamari ne.
Bayan faruwar hakan ne sai jarumi Aliyu Muhammad da akafi sani da Ali Artwork ya fito ya bawa Naziru Sarkin Waka hakuri kan irin abubuwan da suka faru Tsakanin shi da Jaruma Nafisat Abdullahi
aliartwork Kayi Hakuri@sarkin_wakar_san_kano Bazasu taba fahimtar ka ba saboda su duniya suka saka a gaba da rashin son gaskiya Allah yana nan a madakata yana jiran kowa damu dasu Allah yasani mun fita hakinsu tunda mun fada musu gaskiya kuma sunki dauka ka bari kawai duniya zata musu wa'azi watarana ko bayan ba ranmu Allah ka kara haska mana gaskiya a duk inda take Allah kabamu ikon binta su kuma Allah ya shiryesu in masu shiryuwane in kuma ba masu shiryuwa bane Allah ka fimu sanin yadda zakai da mu dasu Allah ka mana KYAKYAWAN karshe Darajar Annabi Muhammadu S.AW S
No comments