DA ALAMA SHAHARARRIYAR YAR TIK TOK MURJA IBRAHIM ZATA FARA FITOWA A WAKOKI DA FINA FINAN KANNYWOOD Duba da irin yadda take bibiyar B...
DA ALAMA SHAHARARRIYAR YAR TIK TOK MURJA IBRAHIM ZATA FARA FITOWA A WAKOKI DA FINA FINAN KANNYWOOD
Duba da irin yadda take bibiyar Babban Mai bada umarni (Director) a Masana'antar Kannywood Sunusi Oscar 442, Murja Ibrahim Tik Tok da alama tana so ya fara saka ta a cikin wakokin Hausa na Kannywood.
Alamu da yawa sun nuna haka sakamakon yadda shahararriyar 'yar tik tok din take ta bibiyar jarumin a shafukan sa na sada zumunta kama daga kan Instagram da sauran su, tana fadar kalmomin yabo a kansa, tare da kirari da kuma addu'o'in ruguza makiyan sa a duk inda suke.
Murja Ibrahim tik tok bata tsaya nan ba domin kuwa har bidiyoyin sa take posting tana kara yabon sa. A cikin bidiyoyin nasa harda inda yake Sallah wai don duk yaji dadi ya fara bata aikin wakokin Hausa na Kannywood kaga kenan shahararta zata zama kashi biyu kenan.
To amma ba a nan Gizo yake sakar ba duba cewa 'yan tik tok daban haka zalika 'yan Kannywood ma daban domin kuwa dukkan su suna gudanar da ayyuka iri daban daban. Shi yasa a wata mahanga muke ganin cewa anya tafiyar zata iya zama daya kuwa ba tare da an sami matsala ba?
Da wannan tambayar ne muke neman jin ra'ayoyin masu sauraren akan sahihanci ko kuma rashin sahihancin lamarin, sai mun ji ku.
YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)🖋️🖊️📖🖊️🖋️
No comments