Izzar So Episode 81 Original Wannan Shirin Na Izzar So Tabbas Ya Dau Zafi zinda Zaku Yadda Zaa Kara Karawa Tsakanin Umar Hassim Da Izzar...
Izzar So Episode 81 Original
Wannan Shirin Na Izzar So Tabbas Ya Dau Zafi zinda Zaku Yadda Zaa Kara Karawa Tsakanin Umar Hassim Da Izzar Inda Har Yanzu Da Ake Neman Wanene Jinin Matawalle Tabbas Wannan Shiri Na Izzar So Yanada Matukar Ksyatarwa Inda Ake Bata Kashi Da Jarumai
Wannan Shiri Na Izzar So Shine Shiri Mai Dogon Zango Da Ya Karade Fadin Duniya Domin A Fina Finan Kannywood Shine Film Na Daya
*IZZAR SO EPISODE 81 SEASON 3*
Sanin kanku ne cewa fim din *Izzar So* shine fim wanda har izuwa yanzu bashi da na biyu a da'irar fina finai masu dogon zango kasancewar har yanzu ba'a sami wani fim din Hausa da ake kallon sa a manhajar fina finai na *youtube* ba domin kuwa yana da dubban daruruwan masu kallo a ko'ina a fadin duniya.
Labarin Izzar So wani salo ne da ya bamban ta daga ilahirin fina fina masu dogon zango da ake nunawa a masana'antar kannywood domin kuwa shine kadai fim din dake nuni akan addinin *Musulunci* ziryan.
A satin da ya gabata dai munga inda abubuwa suka sake dagulewa ta kowane sashe inda a bangaren *Hajara* diyar *Matawalle* mamanta take nuna fushi dangane da abin da taje tayi a babbar ma'aikata inda Hajara ta rarrashi mahaifiyar tata sannan ta nuna mata abinda yake faruwa na yunkurin rusa babbar ma'aikata.
A bangaren *Hajiya Sarah* nan ma al'amura suna kara rincabe mata yayin da ta sha alwashin cewa baza ta bari *Hajara* ta nemi aiki a ofishin da *Umar Hashim* ya bari ba saboda gudun tashin tashina.
Bangaren *Hajiya Nafisa* shine bangaren da yafi kowane sashe rikicewa inda aka sanar wa da Hajiiya Nafisa cewa ya kamata ta taka a sannu domin kuwa nata yazo karshe inda Hajiya Sara ta sanar da ita cewa ita fa ba diyar *Matawalle* bace 'year mtsintuwa ce...
...al'amarin da ya dagulawa kowa lissafi harda yan kallo ma domin a halin yanzu kowa ya zura ido yaga me zai biyo baya...
Idan baza ku manta ba a a baya *Hajiya Nafisa* ta yi wata magana da take nuni da cewa a shirye take ta kawar da *Matawalle* domin gaje dinbin dukiyar da Matawalle yake da ita.
Sannan kuka a yaune ake sa ran bayyanar *Aliyu* babban dangidan *Matawalle* da ya bata tun yana karami... Kai bari dai in takaice maka cakwakiya iya cakwakiya.
Kuci gaba da sauraron mu don kawo muku wasu dadadan labarai daga sassan duniya.
Sai Anjima.
*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON)*
No comments