IZZAR SO EPISODE 83 Wai shin Izzar So wanne irin fim ne kuma wadanne irin mutane ne a cikin wannan kafacen?Wannan wata tambaya ce da wan...
IZZAR SO EPISODE 83
Wai shin Izzar So wanne irin fim ne kuma wadanne irin mutane ne a cikin wannan kafacen?Wannan wata tambaya ce da wani ma'abocin kallon fim din na izzar so yayi wa wakilin mu.
Ya kara dacewa "shifa nema ake yi a karar masa da ruwan kansa da kuma hakurin sa baki daya" yace "ya lura idan aka dauko hanyar warware matsalar sai kuma kaga an sake shiga wata sarkakiyar da babu wata salãma a cikin ta ko kadan.
Ya ce " fim din Izzar so baya yiwa masu kallo dadi a halin yanzu saboda karancin nasarar da gaskiya take da shi, kasancewar masu makirci da tuggu da cuta da zalunci sune suke cin karen su babu babbaka, inda hakan yana kuntatawa masu kallo. Haka ne ma yasa da yawa suka ce sun sawwakewa kansu wannan jidali domin kuwa abin baya musu dadi wai ace koda yaushe mugaye ne suke takurawa mutanen kirki, wannan wane irin abu ne?
Ya kamata a bawa Umar Hashim da tawagarsa ta mutanen kirki dama suma su shimfida rayuwar adalci a wannan masana'anta sannan su kuma maha'intan da suka rage a tabbatar sun ci gidan su domin nunawa sauran maha'inta makomar su hakika.
Amma a Izzar so wani abu da yake faruwa, ya kasance koda an bankado rashin gaskiyar mutum to fa a karshe yaci bulus saboda baya karbar horon ha ya dace da shi, maimakon haka ma wai sai a bullo masa da wata sabuwar dama ta wani waje da zai ci gaba da gallazawa masu gaskiya.
Hakan yana yiwa masu kallo ciwo kwarai da gaske domin Izzar so yana bawa mugaye damar mike kafa suyi ta cin karen su babu babbaka a zahiri domin kuwa azzalumi zaiji cewa ashe akwai wata sabuwar hanya da zai bullo domin gujewa tozarta.
Hajiya Sara, Hajiya Nafisa, Jibrin, da sauran 'yan tawagar su kowa yaga abin da ya faru dasu na tonon silili akan irin tabargazar da suka shafe lokaci mai tsawo suna tafkawa amma sai gashi shirin Izzar so yana kokarin sake bullo musu da wata hanya domin ci gaba da ta'asar su.
Wai ina Izzar So ya dosa ne? Domin an hana duk wani mai gaskiya tasiri a cikin sa, ita kanta diyar Maigirma Matawalle (Hajara) nema ake a dakile tasirin ta duk da cewa mafi yawancin masu kallo sun dora fatan su akanta cewa ba shakka zata taka rawar gani ta fuskar tunbuke da kuma jijjige karya da makaryata sai gashi itama ana shirin raunana tasirin ta.
A karshe dai ya karkare da yin kira ga Mai bada umarnin (director) wannan shirin na Izzar So Nura Mustafa Waye da yayi taka tsantsan wajen domin gudun fitar da soyayyar wannan fim mai farin jini daga zukatan masu kallo don Allãh🙏🏼.
Insha Allahu zamu ci gaba da kawo muku dukkan abubuwan dake faruwa dangane da wannan fim mai farin jini wato IZZAR SO.
Ku Saurare mu nan da karfe 9 zamu sako muku videon Izzar so Episode 83
YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)🖋️🖊️📖🖊️🖋️💪🏽💪🏽
No comments