Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

LILIN BABA ZAI SAKI SABUWAR WAKA RANAR SALLA AMMA BA A GA UMMI RAHAB BA

  LILIN BABA ZAI SAKI SABUWAR WAKA RANAR SALLA AMMA BA A GA UMMI RAHAB BA Shahararren mawakin Hip Hop da R&B Lilin Baba ya bayyana a...

 LILIN BABA ZAI SAKI SABUWAR WAKA RANAR SALLA AMMA BA A GA UMMI RAHAB BA

Shahararren mawakin Hip Hop da R&B Lilin Baba ya bayyana a allon sanarwar shafin kafar sada zumunta ta Instagram cewa zai saki wata zazzafar sabuwar waka a ranar sallah.

Sai dai ganin hoton wata yarinya daban wadda ba Ummi Rahab ba sai mutane suka fara tsegume tsegume kan cewa shin wai me ya faru ba'a ga Ummi Rahab ba.

Ummi Rahab dai itace matashiyar jarumar da labarin ta ya yamutsa hazo a watannin baya sakamakon dangantakar ta da Adam A Zango wadda tayi tsamari har takai aka sami sabani.


Daga baya ne aka gano cewa ita wannan kyakykyawar matashiyar jarumar tana soyayya da fitaccen mawaki Lilin Baba wanda shine wanda yake daukar nauyin fim mai suna Wuff. Fitowar Lilin Baba ke da wuya ya dagulawa Adam Zango lissafi sakamakon kasa shi da aka yi.

UMMI RAHAB

A halin yanzu dai mutane suna nan suna dakon fitowar wannan sabuwar wakar daga Lilin Baba.

Allah ya nuna mana ranar wannan sallah lafiya.

YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)🖋️🖊️📖🖊️🖋️💪🏽💪🏽💪🏽

No comments