IZZAR SO EPISODE 84 ORIGINAL Masha Allah Izzar zazo Kashi Na 84 A Inda Yau Zamu Kawo Muku Shi Yadda Zara Kasance A Izzar So Kadan Daga...
IZZAR SO EPISODE 84 ORIGINAL
Masha Allah Izzar zazo Kashi Na 84 A Inda Yau Zamu Kawo Muku Shi Yadda Zara Kasance A Izzar So Kadan Daga Ciki Inda Zamu Nuna Muku Film Din Izzar So Film Ne Mai Dogon Zango Da A Yanzu Babu Kamar Sa A Fadin Arewa Kaf A Kafar YouTube Domin Kuwa Ya Zama Madubin Dubawa Na Fina Finan Hausa A Wannan Lokaci Duba Da Yadda Ake Kallon Film Din Film Din Ya Samu Karbuwa Sosai Da So sai Domin Kuwa Munyi Raayoyin Masu Kallo Film Din Inda Suke Bayyana Raayinsu A kan Film Din
Kamar Haka
Amma a Izzar so wani abu da yake faruwa, ya kasance koda an bankado rashin gaskiyar mutum to fa a karshe yaci bulus saboda baya karbar horon ha ya dace da shi, maimakon haka ma wai sai a bullo masa da wata sabuwar dama ta wani waje da zai ci gaba da gallazawa masu gaskiya.
Hakan yana yiwa masu kallo ciwo kwarai da gaske domin Izzar so yana bawa mugaye damar mike kafa suyi ta cin karen su babu babbaka a zahiri domin kuwa azzalumi zaiji cewa ashe akwai wata sabuwar hanya da zai bullo domin gujewa tozarta.
Hajiya Sara, Hajiya Nafisa, Jibrin, da sauran 'yan tawagar su kowa yaga abin da ya faru dasu na tonon silili akan irin tabargazar da suka shafe lokaci mai tsawo suna tafkawa amma sai gashi shirin Izzar so yana kokarin sake bullo musu da wata hanya domin ci gaba da ta'asar su.
Don Haka Masoyan Shirin Sun Nuna Raayinsu Akan Film Din Da Kuma Yadda Directors Suke Gudanar Da Film Din Suna Fifita Karya Akan Gaskiya Wannan Shine Gaskiya Batu Bayan Kuma Ba Haka Yakamata Ayi Ba
No comments