Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

IZZAR SO EPISODE 84 ORIGINAL

  IZZAR SO EPISODE 84 Lamarin fim din Izzar So ya kara girmama duba da yadda al'amura a gidan Maigirma Matawalle suka kara ta'az...

 

IZZAR SO EPISODE 84

Lamarin fim din Izzar So ya kara girmama duba da yadda al'amura a gidan Maigirma Matawalle suka kara ta'azzara komai kara dagulewa yake kuma ta kowacce fuska, baga matar Matawalle, 'ya'yan sa, maaikatan sa ba, hatta 'yan aikin gidan sa, ina nufin masu share share, wanke wake, girke girke da sauran aike aiken gidan kowa ya wasa wukar sa wai sai an kai Matawalle (Ali Nuhu) kasa an dasa wa dukiyar sa wawa.

Wannan fim Izzar so fadakarwa ce kai tsaye tare da ankarar da masu hannu da shuni akan cewa ya kamata su dinga yin taka-tsantsan wajen tara ma'aikata da kuma dukkan abokan mu'amala.

Abin da yake faruwa a rayuwar yau mafi yawancin mutane a yau shine ya kasance idan ka janyo mutum a jiki domin ka tallafa masa, daga ya sami wajen zama sai ya fara kai maka farmaki ina nufin hare-hare ta ko'ina wai don ya mallake dukiyar ka...kaji butulci.

Abin ma da zai kara baka mamaki kuma ya kara daga maka hankali shine su wadannan mutane sa kake rike dasu baka rage su da komai ba kana tallafa musu iya iyawar ka amma su a wajen su ta ciki na ciki.

Hajiya Sarah dai matar Maigirma Matawalle misali ce akan haka domin kuwa kai da ganin ta kasan tana morewa ma'ana tana more rayuwar ta cikin jindadi fantamawa da kasaita amma hakan duk bai ishe ta ba burin ta sai taga bayan Mijin nata domin mallake dukiyar sa ta kowacce hanya.

Sannan kuma ga Hajiya Nafisa diyar Matawalle itama ba'a barta a baya ba domin baya ga izza da take nuna wa ta hanyar musgunawa mutane da ci musu mutunci a karshe itama ta dukufa wajen ganin ta kawo karshen rayuwar Maigirma Matawalle wai duk don ta mallake masa dukiya, kai jama'a.

Da alama Allah Ya dawo da diyar Matawalle Hajara domin ta zama silar ceto mahaifin ta daga cikin kangin makusanta maciya amana.


Sannan a bangaren Hajiya Sara suna ta cuku cukun kawo masa wani mutum daga waje a matsayin dan sa da ya bata tun yana yaro. Bayan haka ta kirkiri ciki tana so ta kawo masa da wai don duk ta mamaye dukiyar sa. Cakwakiya iya cakwakiya. Allah Ya Kyauta.

Muna nan dai muna jiran fitowar Episode na 84 a yau domin muga yadda zata kasance a tsakanin su.


                             

                            YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)🖋️🖊️📖✍🏽📖🖊️🖋️✍🏽 

No comments