Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Ko Banza Dai Nasan Jinin Wasu Ya Hau Acewar Naziru Sarkin Waka

 Ko Banza Dai Nasan Jinin Wasu Ya Hau Acewar Naziru Sarkin Waka A yau Talata Ne Aka Buda Ball Mai Zafi Na Real Madrid Inda Akai Ta Tafka M...

 Ko Banza Dai Nasan Jinin Wasu Ya Hau Acewar Naziru Sarkin Waka

A yau Talata Ne Aka Buda Ball Mai Zafi Na Real Madrid Inda Akai Ta Tafka Muhawara Tsakanin Sa Da Maniyansa A Shafin Twitter Inda Sukai ta Bata Kashi Da Juna Kamar A Filin Bakl Din

Naziru Sarkin Waka

 










X

*KO BANZA DAI JININ WASU YA HAU*

---Naziru Sarkin Waka

A babban wasan da aka buga ranar talata tsakanin Real Madrid da Kuma Chelsea FC wato wasan kusa da na kusa dana karshe wasan ya dauki hankali sosai ganin yadda reshe yaso ya juye da mujiya.


Naziru Sarkin Wakar San-Kano na daya daga cikin wadan da suka kalli wasan kuma yayi magana a shafin sa na twitter wadda ta yamutsa hazo inda yake cewa *"Ko Banza dai Nasan Jinin Wasu Yau"* wato dai an kadawa wasu hanta kenan.


Sakin wannan bayanin keda wuya sai magoya bayan Real Madrid suka ce dawa Allah Ya hada su domin kuwa sunyi ta mayar da kalaman ramuwa ta hanyan nuni kan cewa *"suna so Naziru ya sani cewa, dakyar nasha yafi dakyar aka kamani"* tare da cin alwashi akan wasan gaba ma sune da nasara.

Wannan dai ba sabon abu bane a fagen kwallon kafa tsakanin sashen magoya baya da kuma tsagin adawa domin zaka samu kowa yana fadin albarkacin bakin sa cikin alfahari da kare kai.

Wasan dai an tashi Madrid na da ci 2 Chelsea nada ci 3 amma dai Real Madrid ce tayi galaba akan Chelsea kasancewar tun farkon wasa a gidan na Chelsea Real Madrid ita ce ta sami nasara da ci 3 da 1. Kaga kenan a yanzu Madrid ya sami tikitin zuwa wasan kusa da na karshe.

Ku ci gaba da bibiyar mu don samun wasu labaran wasannin da dumi dumin su.

*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)🖋️🖊️📖🖊️🖋️*

No comments