TOHFA Murja Ibrahim Ta Turawa Da Ganduje Budaddiyar Wasika Tofah Duba Da Yadda Yanzu Abubuwa Ke Faruwa A Kano Da Wajan Kano Na Barkwanci...
TOHFA Murja Ibrahim Ta Turawa Da Ganduje Budaddiyar Wasika
Tofah Duba Da Yadda Yanzu Abubuwa Ke Faruwa A Kano Da Wajan Kano Na Barkwanci Da Sauran Abubuwan Rayuwa Fitacciyar Jarumar tik Tok Da Kuka Fi Sani Da Murja Ibrahim Tayi Wani Dogon Video Mai minti 3 zuwa 4 Ina Tayi Barkwanci Turawa His Excelenvy sako Inda Take Cewa
Shahararriya Kuma sananniyar 'yar tik tok watou Murja Ibrahim Kunya aikawa gwamnan Kano Umar Ganduje Budaddiyar wasika inda take miko gaisuwa ga daukacin masoyan ta bayan sallama tare da fada musu halin da take ciki a watan azumi.
Murja ta roki wata alfarma gareshi gwamnan na Kano bayan ta yiwa Kano kirari wanda yake nuni da cewa Kano fa ita ce lamba daya a duk fadin Nijeriya inda ta tara abubuwan alfahari kamar su Gadoji (bridges), sannan Kuma tace Kano fa itace dandalin ko Kuma matattarar ariziki a kaf Nijeriya domin kuwa a Kano Aliko DanGote yake ba a wani gari ba sannan idan zafin kai mutum yake takama dashi to fa idan ya fado hannun su Murja anan zai ga tsantsar tijara.
Murja bata tsaya nan ba inda taci gaba da neman alfarma a wajen gwamna Ganduje cewa zata yi baki daga kasar Amerika wadanda kawaye ne a gare ta Kuma ta gaya musu cewa a Kano za'a sauke su don itace al-Jannar Nijeriya za Kuma su zo ne indan sallah ya rage saura kwana Altar mattace tana so itama ayi mata wata alfarma domin kauyen su ba hanya mai kyau shi shine take neman itama a je a yi musu irin gadar (bridge) nan mai dankaren kyau tare da fentin tutar Nijeriya domin bakin nata su kiyaye ta.
Neman alfarmar nata bai tsaya nan ba domin kuwa ta nemi 'yan Hisbah su dan tsagaita musu zuwa kwana hudu inda zasu karkare duk wata kwalisa tare da kwajen ta 'yan Amerika wadan da tun farko tace sufa kawayen nan nata *Ajeboters* ne Kuma gasu jajayen fata.
A karshe ta yi kira ga masoyan ta cewa kada su damu da cewa ta koma kauyen su ko wani abu zai same ta na daga yunwa ko wata matsala, sai aka ga Murja ta kukuta hannunta cikin zanen ta yayin da ta fito da wasu kudade tana cewa kada su damu domin da kudin ta a jikinta baza ta yunwata ba balle ta rame, ta kuma yi musu albishir cewa zata dawo ta same su alhali tana *BULBUL.*
Jakadiyar Arewa Gidan Labari. Ku biyo mu domin jin wasu sababbin labarai, sai anjima.
*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)🖋️🖊️📖🖊️🖋️
No comments