Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Murja Yar Tik Tok Tayi Tofin Ala Tsine Akan Gwamnatin Buhari

  Murja Yar Tik Tok Tayi Tofin Ala Tsine Akan Gwamnatin Buhari X Tofah Abin Ya Ya Fara Kaiwa Mukara Tunda Mukaga Jaruman Wato Fitattun Y...

 

Murja Yar Tik Tok Tayi Tofin Ala Tsine Akan Gwamnatin Buhari X

Tofah Abin Ya Ya Fara Kaiwa Mukara Tunda Mukaga Jaruman Wato Fitattun Yan Tik Tok Sun Fara Tsoma Baki Akan Akan Abubuwa Da Ya Shafi Nigeria Yakamata Gashidai Ana Ta Sala Baki Inda Mukaga Jarumar Tik T tatsoma Baki

Yakamata A gyara Dikinttsoron Kasa


*SHAHARARRIYAR YAR TIK TOK MURJA IBRAHIM TAYI ALLÃH WADAI DA SALON MULKI IRIN NA BUHARI*


Ba safai ake samun yan tik tok suyi magana akan mulki ko masu mulki ba ko kuma yadda suke tafiyar da shugabancin su ba, asali ma dai harkar gaban su kawai suke yi.


Sai gashi matsam wata fitacciyar kuma sananniyar 'yar tik tok mai suna *Murja Ibrahim* tayi tofin Ala tsine a kan salon mulki irin na Buhari shugaban Nijeriya inda tayi masa kaca kaca, irin maganar nan ta Hausawa wato *"wankin babban bargo".* dama kuma ance *"tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka".*


Murja tik tok tayi fata fata da Gwamnatin Buharin ne ta hanyar bayyanar zaluncin sa da gazawar sa ta ko'ina inda aka mayar da rayukan al'ummar wannan kasa tamkar rayukan kiyashi musamman ma yankin Arewa inda nan ne bangaren da suka fi mara masa baya lokacin zabe aka zuba masa kuriar da ba'a taba zabar wani mutum da ita ba a babban zaben kasa. Sai gashi kash! Maimakon ya sakawa mutanen wannan yankuna da alheri abin bai zama haka ba saima karin tsanani da rashin tallafi ga wannan al'umma.


Murja Ibrahim yar tik tok da sauran al'ummar kasa sun yi ala wadai da irin yadda yan Nijeriya suke fama da matsin lamba ta ko'ina daga gwamnati tun daga shugaban kasa, gwamnoni, yan majalisu, ministoci, daraktoci da sauran masu fada aji a dukkan matakan iko a kasar nan, inda suke nuna halin ko'in kula ga dukkan halin matsi da ake ciki a Nijeriya.


Gwamnarin Buhari ta janye duk wani tallafi da talakan Nijeriya yake samun sauki ta kuma kira mutanen Nijeriya da kalmar *Cima Zaune* kalmar da ta batawa mutanen Nijeriya rai.


A baya bayan nan aka sami malami wanda limami ne wani Masallacin Jumaa a garin Abuja ya fadawa gwamnatin Buhari gaskiya akan kisan kiyashi da ake wa yan Nijeriya amma ko a jikin sa, saima dai cewa da yayi wai sun yi ala wadai da faruwar abin.


Kuci gaba da biyo mu a kafafe da shafukan zamani domin samun wasu zafafan labarai da a wajen mu kadai ake fara samun su.

Sai Anjima.

*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON)*

No comments