Mai Horas Da Ƴan Wasan Kwallon Kafar Najeriya Ne Ya Cuce Mu A Wasan Najeriya Da Ghana, Cewar Jarumar Fina-finan Kannywood, Rayya Jaru...
Mai Horas Da Ƴan Wasan Kwallon Kafar Najeriya Ne Ya Cuce Mu A Wasan Najeriya Da Ghana, Cewar Jarumar Fina-finan Kannywood, Rayya
Jarumar Kannywood, Surayya Aminu, wadda aka fi sani da Rayya Kwana Casa’in ta ce kocin Najeriya ne ya cuci kasar a wasanta da Ghana.
A ranar Talatar da ta gabata ce Najeriya ta buga wasan neman shiga Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi bana a Qatar, inda suka tashi kunnen doki.
Hakan dai ya sa Najeriya ba za ta buga wasan cin kofin ba.
A cewar Rayya, “Allah Ya isa ba mu yafe maka ba. Kocinmu ne ya cuce mu. ’Yan Ghana sun sako zaratan ’yan wasansu, amma mu zaratan ’yan wasanmu ba su shigo fili ba. Allah Ya isa! Abdullahi
Shehu, Ahmed Musa, Sadiq Umar, Zaidu Sanusi, Allah Ya yi muku albarka Ya saka muku, mun ga abin da aka muku.”
Rayya ta je har filin wasan domin kallon wasan, wanda hakan ya sa rashin nasarar ya yi mata zafi matuka.
No comments