Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

WAI MENE NE DAMUWAR KU AKAN SAI NAYI AURE? ---Nafisa Abdullahi

  WAI MENE NE DAMUWAR KU AKAN SAI NAYI AURE? ---Nafisa Abdullahi Magana akan sai nayi aure kafin na fadi wata magana mai dangantaka da w...

 

WAI MENE NE DAMUWAR KU AKAN SAI NAYI AURE?
---Nafisa Abdullahi

Magana akan sai nayi aure kafin na fadi wata magana mai dangantaka da wannan. Tambaya ta anan shine "Mene ne dangantakar maganta da aure na?" Tayi Murmushi sannan ta kara da cewa "A yau idan nace bazan yi aure ba, babu wani mataki da zaku iya dauka akan hakan... Kunga kenan ra'ayoyin ku a kan sai nayi aure sun tashi A BANZA KENAN!

Anan ma anyi ta dauki ba dadi dangane da wannan dan tsokaci da jaruma Nafisa Abdullahi ta yi inda aka yi ta gutsiri tsoma. Kasancewar Nafisa Abdullahi wallafa wannan kalamai ne da harshen turanci suma masu mayar da martani abin da suka yi kenan.

Misali: Aminu Garba Umar @Asquare... Replying to @NafisatOfficial

" Abin da kika fada gaskiya ne amma ki sani ita fa gaskiya daci ne da ita. Amma ki sani duk masu bambancin ra'ayi da naki to fa za su taso miki ne haikan da maganganun su sai dai ki toshe kunne. Domin kuwa mutanen Arewa ne suke yin aure aure kuma suke haihuwar yara da yawa.

Mustafa Ibrahim @MustyIb... Replying @Asquare... "Alaji Allah ne yache ayi auren ba Northerners ba. In kuma zaka ja da maganar Sa toh, kaga sai inyi shiru.

Shi kuwa Ahmad Muhammad Adam @Fr... Replying to @HusaynahRCHP da @NafisatOfficial cewa yayi "Ba maganar gori bane, kuyi tunani da kanku mana, Allah wani Wanda bashi da auren yafi wanda yake dashi sanin manufofin auren dama sanin meye auren. Da yawan samari da yammata suna shiga jami'ar aure ne ba tare da  sunyi ko da nursery ba bare firamare a cikin aure.

Abdullahi Abdul'aziz Goma @... Replying to @freshman1440 da @HusaynahRCHP da @NafisatOfficial cewa yayi "Ciki harda Nafisa Nafisa Abdullahi ko

SA'A @HussainiSaadatu... Cewa tayi " Ita tambayar ta anan ita ce "Shin wai aure dole ne a Musulunci... Ba Dole Bane da babbar murya, Aure samun dama ne... Muna karanta Al-Qur'ani amma muna danne gaskiya...

Insight @AbdulbasitMjos... Cewa yayi " Aure ba dole bane matukar zaka iya tsare kanka daga zina.

Naz @M_Nazeer... Replying to @NafisatOfficial Cewa yayi "Gaskia Twitter kuna hadawa jaruman kannywood mata zafi domin kuwa a IG da Facebook tamkar bauta musu ake yi ma.

Shi kuwa _Khalid @MusaSayyf... Replying to @NafisatOfficial Cewa yayi "Mafi yawancin mata masu magana a wannan shafi basu da cikakkiyar wayewa akai shi yasa a iya matakin su suke ganin cewa su shaharru ne, gasu nan muna ganin su kullum.

 Bashir Bature @BashirB_ "Wannan shine Alaramma Abdullahi Getso ya haddace Kur'ani yana da karancin shekaru.

Yayi aure yana da shekara 16. Yana da ilimin Fiqihu da Qira'a. Sannan kuma yana iya karanta ilahirin Qur'an daga Baqarah har Nasi babu kuskure. Wadanda suka sanshi zasu tabbatar muku da haka.

Allah Ya Kara masa lafiya da imani da mu duka baki daya. Ameen🙏🏼

To Allah Ya sa mu dace wannan shine kadan daga cikin abin da kalaman jaruma Nafisa Abdullahi suka haifar. Allah Ya Kyauta.

Ku ci gaba da bibiyar mu domin jin wasu labaran kuma.

Nafisa Abdullahi

YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)🖋️🖊️📖🖊️🖋️💪🏽💪🏽💪🏽

No comments