Boyeyyen Siri Da Baku Sani Ba Game Da Dauda Kahutu Rara Assalamu Alaikum jama,a zan danyi wani sharhi akan wannan bawan Allah dangane ...
Boyeyyen Siri Da Baku Sani Ba Game Da Dauda Kahutu Rara
Assalamu Alaikum jama,a zan danyi wani sharhi akan wannan bawan Allah dangane da irin sauya lissafin masana,antar shirya fina finai da yayi a lokacin da yan masana,antar da yawa suka yanke kauna da sana,ar a matsayin abinda zai rike su
Dauda Adamu kahutu kowa yasan ba dan film bane a farkon tasowar daukakarsa, sannan kuma ba film ne ya taimakeshi gurin shahararsa ba, Haka zalika babu wani dan film dazaice shine yai tallan DAUDA har duniya tasanshi ba, Kuma ina da tabbacin idan bai jingina da film ba kowanne irin buri nasa zai cika na bangaren layinsa na siyasa ,
To amma meyasa yazama garkuwa ga wannan masana,anta? Meyasa yake samo kudinsa a harkarsa ta siyasa da gwamnati ya kawowa cikin masana,antar? Amsa shine tausayi da karamci da kaunarsa ta tsamo yan masana,antar da ga cikin bakin talaucin da juyin juya hali da kura tsira dana bakinki ya Jefa masana,antar,
DAUDA shine daya tilo daya fara karfafa gwiwar mawaka da makada da yan rawa ta hanyar dawo musu da tunanin su jikinsu game da sana,ar da suke wanda a da sunfara yanke kauna da ita ,
DAUDA shine wanda yafara saka kowacce irin gasa domin amfani da wannan damar gurin tallafawa yan masana,antar tare da saka kyautuka kala kala wanda haka yasaka wasu suka gani suka kwaikwaya wanda ayau duk wanda yasamu irin wannan farin cikin yana da Lada na sunnanta kyakyawan aiki,
DAUDA shine wanda ya nunawa yan masana,antar cewa su shiga siyasa sukuma zama masu amfani da baiwar da Allah yabasu ta kirkira domin zama tare da gwamnati don cimma manufa ta taimakon masana,antar wanda hakan yai sanadin dayawa suka samu damammaki a gwamnatance daga jahohi har Birnin tarayya Abuja
DAUDA shine mutum na farko dan cikin masana,antar daya fara empowerment ta hanyar bada ababen hawa kama daga MOTA BABUR DA KEKE NAPEP dss badon komai ba said saidon karfafa gwiwa ta matasa dake masana,antar
DAUDA shine wanda ya fara yunkuri na tunawa da tsoffin yan masana,antar wanda duniya ta manta dasu ta hanyar tallafa musu lokuta daban daban tare da kirkira
Allah kabamu damar dazamu taimaki na kasanmu
No comments