Buhari Yaki Magana Akan Kisan Deborah Amma Yayi Magana Akan Akashe Mutane Akan Abubuwa 10 X A shekarar 2019 Maigirma Shugaban Kasa Muh...
Buhari Yaki Magana Akan Kisan Deborah Amma Yayi Magana Akan Akashe Mutane Akan Abubuwa 10
A shekarar 2019 Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace duk wanda aka samu da laifin ya saci akwatin zabe a harbeshi har lahira
A shekarar 2021 Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace duk wanda aka kama yana rike da bindiga kirar AK47 a harbeshi har lahira
A wannan shekara na 2022 Shugaban Kasa Buhari yayi Allah wadai da wadanda suka zartar da hukuncin Qattalawa akan wacce ta yiwa Annabi (SAW) batanci
Mun san cewa Nigeria hadin gambiza ce, akwai Musulmai da wadannan ba Musulmai ba, to amma a matsayinka na Musulmi baka da wani uzuri a gaban Allah da zai hanaka bawa addininka kariya don tsoron wasu ko tsoron gushewar mulki
Buhari ba wanda zai cireka daga mulki don kayi gum da bakinka, ka sanida wadanda suka baka shawara ka fitar da sanarwan Allah wadai da hukuncin, da wadanda kake kokarin ka faranta musu rai ba zasu iya kareka a gaban Allah ba
Akan ka kalubalanci wannan hukunci da aka zartar kan wacce tayi batanci yafi maka alheri ka ajiye mulkin idan ma kana ganin cewa don Kasar hadin gambiza ce
Akan kare Demokaradiyyah kace a kashe duk wanda ya saci akwatin zabe, sannan kace a kashe duk wanda aka gani yana rike da AK47, to duk wannan bai kai ko kusa da darajar Annabi (SAW) ba
Gashi ka tsufa, kana kusa da kabari, ni banga wani abinda ya rage maka da zakayi mai muhimmanci fiye da riko da Musulunci ba domin ka hadu da Allah lafiya
Ya kamata mu kasance masu fifita addinin mu na Musulunci akan komai na rayuwar duniya, riko da Musulunci shine ribar da zamu samu anan duniya da kuma lahira
Allah Ka taimakemu
No comments