Innalillahi Wa Inna llaihi Raji'un. An Kashe Wata Musulma Mai Juna Biyu Tare Da Yayan Ta Su 4 A Jihar Anambara. Yan Najeriya da d...
Innalillahi Wa Inna llaihi Raji'un. An Kashe Wata Musulma Mai Juna Biyu Tare Da Yayan Ta Su 4 A Jihar Anambara.
Yan Najeriya da dama sun kufula, sun kuma fusata akan kisan mace mai ciki da yaya hudu Na jihar Anambra -Jama'a da dama a shafukan sada zumunta musamman yan arewacin Najeriya.sun fusata sakamakon wani bidiyo da ake ta yadawa da ke nuna yadda aka kashe wata mata da yara a Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.
Wasu da ake zargin yan kungiyar IPOB ne sun kashe matar mai suna Harira Jibril, mai shekara 32, da yayanta Fatima, mai shekara tara, da
Khadijah, mai shekara bakwai, da Hadiza, mai shekara biyar, da Zaituna, yar shekara biyu da wasu akalla mutum shida a jihar.
BBC ta tattauna da mijin matar mai suna Jibril Ahmed wanda a cewarsa matar- tasa wadda ke dauke da cikin wata tara na hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai tare da yaransu 0rumba North wanda a hanyar ne aka tare su aka kashe su.
Alhaji Usman Abdullahi wanda shi ne Sarkin Hausawan Ihiala a Anambra shi ma ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce matar asalin yar Jihar Adamawa ce daga arewacin Najeriya.
Sarkin Hausawan wanda yanzu haka yake gudun hijira ya ce aľ'ummar Hausawa na cikin wani hali a Jihar Anambra. A cewarsa, a Karamar Hukumar Ihiala wanda a nan yake, babu wani Bahaushe da ya rage sakamakon duk sun yi gudun hijira saboda barazanar yan Kungiyar ta IPOB.A |Ko a kwanakin baya sai da wasu da ake zargin yan kungiyar IPOB ne suka kashe wasu sojoji biyu da suke shirin yin aure a Jihar Imo.
Yan Najeriya da dama sun fusata kan wannan lamari inda da dama ke kokawa kan yadda jaridun kasar da dama suka ki daukar wannan labari da muhimmanci ko kuma bibiyarsa. Wasu alamu sun tabbatar da cewa wannan kashe-kashen da yan Kudancin Najeriya musamman Inyamurai suke wa yan Arewacin kasar, baya rasa nasaba da daukar fansa akan
kisan Deborah Samuel, wato. dalibar nan da ta zagi Manon Allah $AW a jihar Sokoto Malam Bini Kasim yayi wani karin haske akan AA wannan al'amari, ga kuma abinda yace
