Ba A Yi Wa Mawakin (S ufin Zamani) Da 'Yan Fim Suka Saka Aka Kama Adalci Ba, Domin Gaskiya Ya Fada A Wakarsa Cewa Mafi Yawan 'Y...
Ba A Yi Wa Mawakin (Sufin Zamani) Da 'Yan Fim Suka Saka Aka Kama Adalci Ba, Domin Gaskiya Ya Fada A Wakarsa Cewa Mafi Yawan 'Yan Fim Mata Ba Sa Iya Zaman Aure.~ A cewar Imam Indabawa Aliyu
A Wakar Sufin Zamani Zan iya lissafo mata 'yan fim sama da guda talatin wadanda suka kashe auransu ko suka kasa zaman aure, amma abu ne mai wahala na iya lissafa mata biyar 'yan fim wadanda suka yi aure suka zauna dakin mazajensu shekaru da yawa.
Ko 'yan fim din ai sun san gaskiya mawakin sufin zamani ya fada musu. Gwara su je su yi aure su daina gagaramba da yawon ta zubar suna lalata tarbiyar al'umma.
Kawai an raina shi ne, sufin zamani shi ya sa aka zalunce shi. Kuma Allah zai saka masa.
No comments