Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Ya kamata duk wani masoyin Atiku Abubakar da Bola Ahmad Tinubu ya nutsu ya karanta wannan rubutun da kyau.....

  Ya kamata duk wani masoyin Atiku Abubakar da Bola Ahmad Tinubu ya nutsu ya karanta wannan rubutun da kyau...... Manyan 'yan jaridu...

 Ya kamata duk wani masoyin Atiku Abubakar da Bola Ahmad Tinubu ya nutsu ya karanta wannan rubutun da kyau......

Manyan 'yan jaridu masu bincike ne suka tattaro dukkannin bayanan, dake dauke da darasin siyasa. Sunyi kokarin tattaro alaka, kamanceceniya da tarayyar da dan takaran APC Bola Tinubu ya yi da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.  Bayanin nasu ya kasu kashi-kashi har kashi 10. Ga bayanan kamar haka;

1. SHEKARU 

A shekarar nan Atiku Abubakar zai cika shekara 76 a Duniya domin a haife shi ne a 1946. Shi kuwa Bola Tinubu a bana ya cika shekara 70 da haihuwa. Kusan dukkaninsu sa’annin juna ne, tazarar shekara biyar ne tsakanin ‘yan takaran. 

2. DUKIYA 

Dukkanin ‘yan siyasan biyu su na da arziki, attajirai ne na buga misali, sai dai Bola Tinubu ya yiwa Atiku Abubakar fintinkau a wurin tara arziki.Tun kafin shigarsa siyasa, Atiku Abubakar ya kai babban matsayi a aikin kwastam, anyi kiyasin yanzu haka ya mallaki kadara ta kusan Tirilan guda. Shi ma Bola Tinubu dan kasuwa ne ko kafin ya zama gwamnan Legas, a yanzu haka anyi kisan ya mallaki kadara ta kusan tiriliyan 4.Tinubu shine dan siyasar da yafi kowane dan siyasa tarin arziki a Najeriya. 

3. FARA SIYASA 

Inda wadannan mutane suka kara yin tarayya shi ne sun shiga siyasa ne kusan a lokaci daya. A 1992 aka fara jin sunan Atiku da Tinubu da kyau a Najeriya. Bola Tinubu ya zama Sanata a lokacin, shi kuwa Atiku ya yi takarar shugaban kasa. Tinubu yana tare da su MKO Abiola, Atiku yaronsu Shehu Yar'adu'a ne. 

4. SAMUN KUJERAR GWAMNATI

Bayan an dawo farar hula a 1999, Wazirin Adamawa da Jagaban suka lashe zaben gwamna a jihohinsu na Adamawa da Legas a karkashin AD da PDP. Bola Tinubu ya yi shekaru takwas yana gwamna, shi kuwa Atiku ya samu damar tafiya Aso Villa. 

5. RASA MADAFAN IKO

Daga watan Mayun 2007 zuwa yanzu, mutanen nan biyu ba su rike wani mukami a gwamnati ba.Shekaru 15 kenan da Atiku Abubakar ya fita daga Aso Villa. Shi ma Bola Tinubu ya bar kujerar gwamnan Legas a 2007, rana daya da abokin takaransa na yanzu. 

6. CIN BURIN MULKI 

Inda wadannan ‘yan takara suka sake yin kama da juna a siyasa shi ne dukkaninsu sun dade su na neman yadda za su samu damar shugabantar Najeriya.

Atiku ya yi takara a 1992, 2007, 2011, 2015, da 2019, yayin da shi kuma Tinubu yake ta jiran 2023. 

7. ZARGIN RASHIN GASKIYA

Ana yi wa ‘yan siyasan biyu kallon marasa gaskiya wadanda suka amfana da baitul mali ko su na kan yi a dalilin kusancin da suka samu da kujerun gwamnati. 

8. AKIDAR SIYASA

Masu nazarin siyasa a Najeriya su na cewa jirgi daya ya dauko ‘dan takaran na jam’iyyar PDP da abokinsa na APC domin duk sun yi imani da tsarin jari hujja. 

9. RASHIN KAUSHI DA RA’AYIN RIKAU KO ADDINI

An tabbatar da Atiku da Tinubu a matsayin wadanda ba su da ra’ayin rikau a kan abin da ya shafi lamarin addini da kabilanci ko yanki. 

Bola Tinubu ya na auren Kirista, Atiku kuwa ya auri Bayarabiya da Inyamura a cikin matansa. 

10. TARAYYA A JAM’IYYA

Kafin su raba jiha a siyasa, Wazirin Adamawa da Asiwaju Tinubu sun zauna tare a karkashin jam’iyyun SDP a 1992, ACN a 2007 da jam'iyyar APC a 2015. Bayan Atiku ya yi takara ne ya bar ACN a 2007, sannan ya sauya-sheka daga APC a 2018. Gareku masoyan kowane bangare, ya rage naka kasan irin siyasar da zaka yi, domin dukkansu kusan halin su daya ne, ba suda wani bambanci a tsakanin su. Kada ka bari siyasar 2023 ta rufe maka ido, ka yita fada da 'yan uwanka ko abokanan ka, akan 'yan siyasar. Kada ka bari a chusa maka kabilanci, ko wani abu na daban da zai sa kaji haushin dan uwanka akan su.

Kowa yabi ra'ayin shi na siyasa, domin ba don lada ake siyasa ba. Babban fatanmu, Allah ya zama mana mafi Alkhairi a garemu, mun barwa Ubangiji zabi shi yafi mu sanin mafi Alkhairi a garemu.


No comments