Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Sin: Ya Dace Amurka Ta Ingiza Hada Kan UNESCO Bayan Dawowarta Hukumar

  Sin: Ya Dace Amurka Ta Ingiza Hada Kan UNESCO Bayan Dawowarta Hukumar Jiya Juma'a 30 ga watan Yulin da ake ciki daga duk fannoni, a za...

 






Sin: Ya Dace Amurka Ta Ingiza Hada Kan UNESCO Bayan Dawowarta Hukumar


Jiya Juma'a 30 ga watan Yulin da ake ciki daga duk fannoni, a zartas da wani daftarin kuduri yayin taron musamman na babban taron UNESCO wato hukumar kula da ba da ilmi da kimiyya da al'ada ta MDD.


Bayan dawowar Amurka hukumar, ya dace ta yi kokari domin ingiza hada kan hukumar, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin hukumar, and maimakon raba kai ko kawo baraka.


Yang Jin ya kara da cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta cika alkawarin da ta dauka, ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, kuma ta biya kudin haraji a kan lokaci, tare kuma da biyar daukacin kudin haraji da ba ta biya a cikin 'yan shekarun da suka gabata ba a kan lokaci.


Amurka za ta samar da tallafin kudi ga hukumar domin gudanar da ayyukan dake shafar tsaron lafiyar manema labarai da ba da ilmi a kasashen Afirka. Bisa kudurin da aka zartas da shi.


Rahotannin da kafofin watsa labarai suka gabatar sun nuna cewa, gaba daya adadin kudin da hukumar UNESCO take binta ya riga ya kai dalar Amurka mil 619.



Ads h