Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Ƴan sanda sun gargaɗi ƴan ƙwadago game da zanga-zanga

 Ƴan sanda sun gargaɗi ƴan ƙwadago game da zanga-zanga Muƙaddashin babban sufeton ƴan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya bayana...

Ƴan sanda sun gargaɗi ƴan ƙwadago game da zanga-zanga


 Ƴan sanda sun gargaɗi ƴan ƙwadago game da zanga-zanga


Muƙaddashin babban sufeton ƴan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya bayana damuwa kan zanga-zangar da ƙungiyyin ƙadago suka shirya yi, inda ya yi gargaɗin cewa ƴan sanda ba za su lamunci duk wani abu da zai kawo rikici ba.


Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce ƴan ƙasa suna da ƴancin yin zanga-zanga kamar yadda kundin mulki ya yi tanadi amma dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.


Rundunar ƴan sandan ta ce a baya irin wannan zanga-zanga tana rikiɗewa ta zama tashin hankali, sabda haka ta ke gargaɗin cewa ba za ta bari a gudanar da duk wani abu da zai kawo matsalar tsaro ba.


ACP Adejobi ya ce duk wani yunƙurin tayar da rikici a lokacin zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago zai fuskanci fushin hukuma.


Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun shirya fara zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewa da soke tallafin mai da gwamnati ta yi.



Ads h