Gwamnatin tarayya za ta sake gurfanar da Emefiele a gaban kotu Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake gurfanar da gwamnan babban bankin ƙasar, ...
Gwamnatin tarayya za ta sake gurfanar da Emefiele a gaban kotu
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake gurfanar da gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele da abokan ƙawancensa da aka dakatar da su, a babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis bisa zargin almundahanar kuɗi har naira biliyan 6.9.
Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa za a gurfanar Emefiele ne tare da wata ma’aikaciyar CBN, Sa’adatu Yaro da kamfaninta mai suna 'April1616 Investment Limited' a kan laifuka guda 20 da suka hadar da damfara, da haÉ—in baki wajen aikata laifi da kuma bayar da cin hanci da rashawa ga abokan huldarsa.
Ba a ji wani bahasi daga jami'an da ake zargin ba, kan sabbin tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Emefiele wanda ke tsare tun lokacin da aka dakatar da shi daga aiki a ranar 9 ga watan Yuni, 2023, an zarge shi da bayar da cin hanci da rashawa ga Yaro.
Laifin ya saba wa sashe 19 na dokokin cin hanci da rashawa da sauran laifukan da suka shafi doka ta 2000.