Matashin da ke neman sauya rubutun Hausa da sabbin harufa Ranar 26 ga watan kowane Agusta - irin ta yau ke nan - ne aka ware domin bikin Ran...
Matashin da ke neman sauya rubutun Hausa da sabbin harufa
Ranar 26 ga watan kowane Agusta - irin ta yau ke nan - ne aka ware domin bikin Ranar Hausa.
Albarkacin wannan rana, mun tattauna da matashi Sadar Musa, wanda ya ƙirƙiri baƙaƙe da wasula na Hasua 37 sababbi fil.
Mazaunin unguwar Dala a birnin Kano na arewacin Najeriya, Sadar ɗalibin Hausa ne a Buɗaɗɗiyar Jami'a ta Ƙasa (National Open University) a Najeriya.
%20(30).jpeg)