Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Trump bai halarci mahawarar 'yan takarar jam'iyyarsa ba

Trump bai halarci mahawarar 'yan takarar jam'iyyarsa ba An fafata a mahawarar 'yan takarar neman shugabancin Amurka na babbar ja...

Trump bai halarci mahawarar 'yan takarar jam'iyyarsa ba

Trump bai halarci mahawarar 'yan takarar jam'iyyarsa ba


An fafata a mahawarar 'yan takarar neman shugabancin Amurka na babbar jam'iyyar adawa ta Republican ba tare da tsohon shugaban kasar Donald Trump ba.

Donald Trump da ke zama dan takara na gaba-gaba a jam'iyyar, sauran 'yan takarar 8 da ke neman tikitin jam'iyyar na bukatar sake lale a kan wanda zai jagoranci Republican a zaben shekarar 2024.


A cewarsu Trump na kara yin bakin jini a kasar kuma ba za su iya tunkarar babban zaben da zai ba su nasara a haka ba.


Gaba a wannan Alhamis Donald Trump zai mika kansa ga mahukunta a Georgia domin fuskantar shari'ar tuhumar da ake yi masa kan zargin yunkurin murde zaben shekarar 2020 a jihar.


Ko a ranar Laraba lawyansa da wasu mutum biyu sun mika kansu ga mahukuntan na Georgia bisa zargin rawar da suka taka a wancan zaben.


Wannan dai shi ne karo na hudu da ake tuhumar Trump tun watan Afrilu, hakan kuma ya sa shi zama tsohon shugaban kasa na farko a tarihin Amurka da ke fuskantar tuhume-tuhume a matakai da dama.




Ads h