Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Tsohon Shugaban Côte d'Ivoire Bedié ya rasu

 Tsohon Shugaban Côte d'Ivoire Bedié ya rasu Shugaban da ya mulkin kasar Côte d'Ivoire tsakanin 1993 da 1999 Henri Konan Bedié da so...

Tsohon Shugaban Côte d'Ivoire Bedié ya rasu

 Tsohon Shugaban Côte d'Ivoire Bedié ya rasu


Shugaban da ya mulkin kasar Côte d'Ivoire tsakanin 1993 da 1999 Henri Konan Bedié da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa ya rasu bayan shekaru 89 da haihuwa.


A cikin sanarwar da babbar jami'iyyar adawa ta PDCI ta fitar, ta ce tsohon shugaban da ba a taba fidda tsamanin zai sake komawa kan madafun ikon kasar ba ya rasu ne a wani asibiti na birnin Abidjan. Tuni da jama'a suka fara taruruwa a kofar gidan marigayin domin nuna alhinin rashinsa.


Marigayi Henri Konan Badié ya yi mulki Côte d'Ivoire a tsakanin shekarun 1993 zuwa 1999 kafin sojoji su hambarar da mulkinsa a juyin mulki na farko da kasar ta fuskanta bayan samun 'yancin kai daga Faransa.Tsohon shugaban kasar ta yammacin Afirka na kasancewa babban abokin hammayar shugaba Alassane Ouattara.



Ads h