An Gano Manyan Mutanen da Ke Daukar Nauyin Ƴan Ta'addan a Najeriya Har su 23 Tare da 3 Ƴan Ƙasar Waje A wani bincike na musamman da g...
An Gano Manyan Mutanen da Ke Daukar Nauyin Ƴan Ta'addan a Najeriya Har su 23 Tare da 3 Ƴan Ƙasar Waje
A wani bincike na musamman da gidan jaridar SaharaReporters ta gudanar, ta gano wasu mutane 23, ciki har da 20 'yan Najeriya da uku (3) 'yan ƙasashen waje, waɗanda ake zargi da haɗa hannu wajen samar da kuɗaɗe da kuma tallafa wa ayyukan ta'addanci, musamman na ƙungiyar Boko Haram.
Rahoton ya bayyana cewa waɗannan mutane sun gudanar da mu'amaloli na kuɗi masu yawan gaske da ke cike da tambayoyi, inda kuɗaɗen suka kai biliyoyin Naira, kuma suna da alaƙa kai tsaye da mutanen da aka riga aka yankewa hukunci kan ayyukan ta'addanci.
Binciken ya nuna cewa tawagar ta ƙunshi shahararrun 'yan kasuwa, dillalan canjin kuɗi (BDC), da kuma ma'aikatan gwamnati, waɗanda ke aiki a cikin jihohin Kano, Zariya, Maiduguri, Gusau, Minna, da Sokoto.
An tattaro cewa hukumomi sun kama waɗanda ake zargin 'yan Najeriya a shekarar 2021, amma daga baya an sake su ba tare da an bayar da cikakken bayani ba.
1. Alhaji Saidu Ahmed (Alh Saidu Gold): Wani ɗan kasuwa ne mazaunin Zariya, Kaduna, wanda aka bayyana a matsayin babban mai ba da kuɗin Boko Haram. An gano asusunsa sun karɓi jimillar kuɗi har Naira Biliyan 4.8, kuma akwai shaidar yawan cire kuɗi a hannu. Yana da alaƙa da mutanen da kotun Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yankewa hukunci, kamar su Surajo Abubakar Muhammad, Ibrahim Ali Alhassan, da Bashir Aliyu Yusuf.
2. Usaini Adamu (Baba Hussaini): Ɗan kasuwa a Kano da ke da asusu 111 a bankuna 9. Mu'amalolinsa sun kai shigar kuɗi sama da Naira Biliyan 43 da fitar kuɗi sama da Naira Biliyan 50. An zarge shi da taimakawa wajen samar da makamai da kayan aiki.
3. Muhammad Sani Adam: Babban mataimakin Alhaji Saidu Gold, mai cinikin kuɗin waje da duwatsu masu daraja a Kano da Yola. Ya yi mu'amalar shigar kuɗi har Naira Biliyan 54.1 da fitar kuɗi har Naira Biliyan 54.4 a cikin asusu 41.
4. Adamu Aliyu Kanoma: Ɗillalin kayan ado daga Gusau, Jihar Zamfara, wanda ke da asusu 83. Ya cire kuɗi a hannu har sama da Naira Biliyan 10 tsakanin 2016 zuwa 2020, kuma yana da mu'amala da abokan aiki 22 na waɗanda aka yanke wa hukunci.
5. Sadiq Garba Abubakar: An tabbatar da shi a matsayin muhimmin jigo wajen ba da kuɗi. Ya canja sama da Naira Biliyan 1.65 ga Surajo Abubakar Muhammad tsakanin 2015 da 2017.
6. Nurudeen Gani Aliyu (Alhaji Nura): Ɗan kasuwa kuma dillalin BDC a Sokoto. Ya yi amfani da asusu 218 wajen sauƙaƙe manyan canje-canje na kuɗi zuwa kamfanin Leaf Tobacco & Commodities, wanda ake zargi da sayan makama.
Rahoton ya kuma bayyana mutane uku (3) na ƙasashen waje waɗanda ke da alaƙa da wannan tawagar:
1. Tribert Rujugiro Ayabatwa (Marigayi): Ɗan kasuwa ɗan Ruwanda kuma dillalin taba sigari. Kafin rasuwarsa a Afrilun 2024, asusunsa sun nuna shigar kuɗi na Naira Biliyan 67. Ya karɓi kuɗi daga Alhaji Nura Gani kuma ya sauƙaƙe canja wurin kuɗi zuwa Afirka ta Kudu da ke da alaƙa da ta'addanci.
2. Paul Nkwaya: Ɗan marigayi Ayabataba, wanda suke haɗa hannu a kamfanin Leaf Tobacco & Commodities. Yana da hannu cikin karɓa da canja wurin kuɗaɗe da ke da alaƙa da ayyukan ta'addanci.
3. Aboubacar Hima (Petit): Ɗan kasuwa ɗan Nijar da aka gano a matsayin dillalin makamai a Abuja. Ya sauƙaƙe canja wurin kuɗi sama da Dala Miliyan 1.19 daga UAE zuwa abokan aikin waɗanda aka yanke wa hukunci.
Bayanan kuɗin, waɗanda suka haɗa da canja wurin kuɗi tsakanin ƙasashe da kuma ambaton da aka yi a hukunce-hukuncen kotun UAE, sun tabbatar da wani haɗin gwiwa ne na tallafa wa ayyukan Boko Haram.
SaharaReporters ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su ci gaba da sanya ido tare da gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya, musamman ganin an saki 'yan Najeriyar da ake zargin a baya ƙarƙashin yanayi mai cike da rudani.
