Wai kun san mene ne ya rusa Adam a Zango A Kannywood kuwa? Wani a sashin tsokaci (comment section) ya ce bai kamata na dinga magana akan ...
Wai kun san mene ne ya rusa Adam a Zango A Kannywood kuwa?
Wani a sashin tsokaci (comment section) ya ce bai kamata na dinga magana akan Kannywood a wannan shafin ba.
Sai dai kuma ni ba magana nake yi akan Kannywood ba, magana nake yi akan masoyina, Adam A Zango.
Duk da cewa komai yana da lokaci, amma shi Adamu kusan za ka iya cewa yarda ce ta karya shi a Kannywood. Ba wai tarihinsa aka birne ba, tsawon zamaninsa aka rage sanadiyyar yarda da ya damƙa wa na kusa da shi. Ko fim zai yi maka to da su za ka yi ciniki, ka gama komai. Su kuma sai abin da suka ba shi.
A kaf Kannywood, Adamu ne ya fara siyawa yaransa motoci. Ya raba wa mutane babura da kuÉ—i. Ya kan iya yin fim guda, ya tattara ribar da ya samu ya ba wa wani yaron nasa domin ya ja jari. A lokacin da Adamu ya koma Kaduna da zama, iya Æ´an Kannywood da suka koma Kaduna da zama Allah ne kawai ya san adadinsu. A lokacin, a gidansa a kullum ana ciyar da mutane sama da 30 abinci sau uku a rana. Sai da ya zama waÉ—annan mutanen komai nasu a jikin Adamu suke samu.
Adamu ya gina mutane, kuma mutane sun ci amanar Adamu. Adamu ba shi da hassada, ba ya nuna ƙyashi, kuma ba ya raina mutane. Amma da yawan ƴan Kannywood sun raina Adamu, sun cutar da Adamu.
Wasu suna cewa wai Adamu ne yake jawo wa kansa maƙiya; wai ya cika surutu akan mahassada. Amma wai kuwa kun san irin rayuwar da Adamu ya yi kuwa? Kun san irin jarabawoyin da ya gani kuwa a rayuwa? Kun san irin tsana da wariyar da aka nuna masa kuwa? Kun san irin sharri da ƙagen da aka yi masa kuwa?
Duk juriyar mutumin nan, akwai lokuta da dama da sai da ya yi kamar zai haukace. Ku tambayi masana lafiyar ƙwaƙwalwa, masu taushin zuciya a cikin irin waɗannan mutanen da suke ganin jarabawa, dandanan suke kashe kansu saboda tarin damuwa.
Abin da mutane da yawa ba su sani ba, masoyan Adamu fa su ne suke riƙe dirkar ɗan ragowar farin cikin da yake samu tsawon lokaci har zuwa yanzu.
Ni na tashi tun yarinta a matsayin masoyin Adamu. Tun ina makarantar firamare nake zana hotunansa ina kafewa a gida da shagonmu. Kuma har yau, da wayona dai ba a taÉ“a yin wani mai shahara “celebrity” wanda nake Æ™auna kamar Adam A Zango ba. Ba na jin kuma akwai ranar da zan daina Æ™aunarsa, saboda kasancewarsa É—an Kannywood bai zama dalilin tursasa ni jingine soyayyarsa ba. Ko ba komai shi Musulmi ne, kuma ba ya nufin kowa da sharri, sannan yana da son cigaban wasu.
Kada ka yi mamaki don ÆŠan’afirka ya so É—an Kannywood, ni na ga malaman addininmu da suke son Æ´an Æ™wallon Turawa, kuma waÉ—anda ba Musulmai ba. Ban faÉ—a da wata manufa ba, na faÉ—a don kafa hujja ne.
