Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Ganduje Na Shirin Sauke Aleebaba Yakasai Akan Maganar Da Yayi Akan Kwankwaso Yafi Kowani Gwamna Aiki

 Wallahi Kwankwaso Ya Fi Duk Gwamnonin Nan Aiki A Jiha, Cewar Ali Baba Fagge  Babban mashawarci ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje akan ...

 Wallahi Kwankwaso Ya Fi Duk Gwamnonin Nan Aiki A Jiha, Cewar Ali Baba Fagge 

Babban mashawarci ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje akan al'amuran addini, S.A Ali Baba Agama Lafiya Fagge, yace dukkan gwamnonin nan da suka matsawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk ya fisu aiki a jiharsa, suna yi masa bakin ciki ne saboda sunga ya fisu farin jini, saboda yanzu dole yana bukatar gidan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje. 

Ali Baba Fagge ya bayyana haka ne a daren jiya cikin wata hira da yayi a rediyo, inda yace shi kansa gwamna Ganduje yana bukatar gidan Kwankwaso, saboda matsi da yake fuskanta daga tsagin tsohon gwamna Sanata Malam Ibrahim Shekarau, wanda yake janye abokan tafiyarsa na tsohuwar jam'iyyar ANPP irinsu Dan Zago, kuma watakila ma akwai wasu yanzu da mukamin gwamnati ne yasa basu bi su ba. 

A yanzu dai an bude wani sabon babin siyasa a Kano, tun bayan ziyarar ta'aziyya da Ganduje ya kaiwa tsohon mai gidansa Kwankwaso, bisa rasuwar kaninsa Alhaji Inuwa Musa Kwankwaso, abinda wasu ke ganin alama ce ta salhu da zai wanzu tsakanin bangarorin guda biyu da aka kwashe tsawon shekaru shida ala taka ledar siyasa.

Ads h