Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

MAI YA HANA ƊAN SARKI DA KWAMANDA RAKA GWAMNA GANDUJE TA'AZIYYA?

  MAI YA HANA ƊAN SARKI DA KWAMANDA RAKA GWAMNA GANDUJE TA'AZIYYA? DAGA Bashir Abdullahi El-Bash A ya yin da mai girma Gwamna Dr. Abdull...

 MAI YA HANA ƊAN SARKI DA KWAMANDA RAKA GWAMNA GANDUJE TA'AZIYYA?

DAGA Bashir Abdullahi El-Bash

A ya yin da mai girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaiwa Kwankwaso ziyarar ta'aziyya bisa rasuwar ƙaninsa Alhaji Inuwa Musa Kwankwaso ya ja hankalin al'umma ciki da wajen Jihar Kano. Wasu na sambarka da hakan wasu kuwa na kushewa.

Sai dai kuma jama'a sun shiga jefa ayoyin tambaya akan rashin ganin fuskar tsohon shugaban jam'iyyar APC na Jihar Alhaji Abdullahi Abbas Ɗan Sarki da kuma kwamishinan ƙananan hukumomi, Hon. Murtala Sule Garo (Kwamanda) waɗanda dukkanninsu makusanta ne na kusa ga gwamna Gandujen amma ba a ga fuskokonsu wajen zuwa ta'aziyyar tare da gwamna ba, koma dai mene ne hausawa na cewa wai ruwa ba ya tsami banza, zuwa gaba ma ji dalili.

Ads h