WACE CE RUKAYYA DAWAYYA? Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da Rukayya Dawayya dai tana daya daga cikin shahararrun taurari kuma jarumai ...
WACE CE RUKAYYA DAWAYYA?
Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da Rukayya Dawayya dai tana daya daga cikin shahararrun taurari kuma jarumai mata da suka yi fice a babbar masana'antar shirya fina finai ta Kannywood dake Nijeriya. Sannan kuma ita ce mamallakiyar kamfanin shirya fina finai mai suna Dawayya Movies Nigeria Limited.
HAIHUWA
An haifi Rukayya Dawayya a ranar 17 ga watan October, 1985 a Unguwar Gyadi Gyadi dake Birnin Kano a arewacin Nijeriya.
Rukayya Dawayya jaruma ce kuma mai daukar nauyin fina finai (producer) duk a masana'antar ta Kannywood.
Rukayya Dawayya na daya daga cikin jarumai mata da suka shahara saboda ta iya fim, gata kyakykyawa sannan kuma ta iya kwalliyar birgewa da jan hankali.
KARATU DA KUMA RAYUWAR TA
Sunan mahaifin Rukayya Dawayya Alhaji Umar Santa wani babban Dankasuwa, sunan mahaifiyar ta Hajiya Fatima. Rukayya Dawayya na da yayye maza su uku sannan tana da kanne mata guda hudu.
Tayi karatunta na firamare a Gyadi-Gyadi a garin Kano, ta kuma gama a shekarar 1990.
A shekarar 1996 Rukayya Dawayya ta je kasar Saudiyya inda ta ci gaba da karatu a wata makaranta mai suna Ummul Qurrah Tahfizul Qur'an inda ta sami shaidar kammala karatunta na nazarin harshen Larabci. Bayan haka ne ta koma Nijeriya kuma ta wuce makarantar Gwamnatin Tarayya dake Kazaure a jihar Jigawa, daga 2000 zuwa 2003.Sannan kuma Dawayya ta sami shaidar diploma a sashen koyon aikin jarida (mass communication) a jami'ar Bayero dake jihar Kano.
A halin yanzu dai Rukayya Dawayya na tare da mahaifiyar ta ne tun bayan rasuwar Alhaji Umar Santa, mahaifin ta.
SHIGAR TA KANNYWOOD
Rukayya Dawayya ta shiga masana'antar Kannywood a shekarar 2000 lokacin da ta dawo daga Saudi Arabia.
Rukayya Dawayya ta fara fitowa a cikin wani fim mai suna Dawayya wanda anan ne ta samo wannan suna da tayi shuhura da shi. Ta kuma taka rawar gani sosai inda hakan ya janyo daraktoci da furodusoshi suka dinga saka ta a fina finan su babu kakkautawa.
Maganar da ake yi da a halin yanzu jarumar ta fito a fina finai sama da 150 inda ta shirya fina finai na kamfanin ta mai suna Dawayya Movies Nigeria Limited.Rukayya Dawayya ta yi fina finai tare da shararrun jarumai kamar su, Ali Nuhu, Sani Danja, Abba Almustapha, Baballe Hayatu, Nuhu Abdullahi, Misbahu M Ahmad da sauran su.
Kadan daga cikin fina finan jarumar:
~Dawayya
~Hajjaju
~Kun yi Sake
~Halimatus Sadiya
~Hawan Hawa
~Ta Fi Su~Ta Isa
~Ummi Sambo
~Nawwara
~Zahra'u Zato Ne
Da sauran su.
A halin yanzu dai Rukayya Umar Santa bata da aure ga mai muradi...
YAKUBU A. ADAM (YACKSON)