Budurwa ta fisge kudi a hannun saurayi Tace A Matsayin Sadakinta A Kano Daga Muhammad Inuwa zaria Wata budurwa ta fisge kudi a hannun saur...
Budurwa ta fisge kudi a hannun saurayi Tace A Matsayin Sadakinta A Kano
Daga Muhammad Inuwa zaria
Wata budurwa ta fisge kudi a hannun saurayinta a lokacin da yake mata gadara da kudin yana ce mata kudin sadakin ta ne shine Allah yabata sa,a ta fisge kudin ta fita da gudu sai gida.
Bisani bata tsaya a ko,ina ba sai gaban iyayenta, ta cewa saura yin tane Wanda take so ya nuna mata cewa wannan shine kudin sadakinta ita kuma ta fisge ta kawo masu.
Yanzu tana rokon iyayenta dasu daura masu aure anan take ta je wajan waliyan shi saurayin tafada masu dansu ya bata kudin sada kinta don Allah suzo a daura aure yanzu.
Bayan saurayin kudin banashi bane na wani abokinshi ne ya bashi ajiya da nufin zaije ya hado kayan lefe na auran abokin nashi, Anadai abun kamar wasa aka daura aure.
Wannan lamari ya farune a karamar hukumar dogowa ta Jihar kano.
No comments