Barauniya Ta Sa Sarkar Miliyan Shadaya Wato 11M A Sunan Yar Jikalle Wato Jikar Ta A 'yan kwanakin nan ne dai aka yi shagalin sunan jika...
Barauniya Ta Sa Sarkar Miliyan Shadaya Wato 11M A Sunan Yar Jikalle Wato Jikar Ta
A 'yan kwanakin nan ne dai aka yi shagalin sunan jikar Hafsat Idris wadda aka fi sani da (Baruniya) shi dai wannan sunan Barauniya ta samo shi be a wani fim din ta mai suna *Barauniya* wanda ta fito tare da jarumi Ali Nuhu da kuma Hauwa Waraka, inda anan ne ta samo sunan.
Ance an cashe matuka gaya a wajen wannan suna inda a nan ne aka hango kakar jaririya ta caba ado da wani leshi mai matukar tsada da daukar ido sannan kuma sanye da wata sarkar gwal da kudin ta ya kai naira milyan 11, inda hakan ya sa kyaun ta ya kara fitowa a fili.
Ance jaririyar taci sunan kakar ta wato Hafsat wanda hakan nema ya karawa bikin sunan armashi.
Hafsat Idris dai ba boyayya bace domin kuwa ta shahara wajen kyau da kuma iya actin a duk sigar da aka fito da ita.
A baya dai in baku manta ba mun baku takaitaccen tarihin jaruma Hafsat Idris (Barauniya). Inda muka fada muku cewa an haife ta ne a garin Shagamu a ranar 19 ga watan February 1984.
Ta kuma shigo masana'antar fina finai ta Kannywood dake arewacin Nijeriya a shekarar 2019 inda ta fara da fim mai suna Barauniya fim din da ya nuna cewa jarumar ta shigo masana'antar ne da kafar dama domin kuwa duk da cewa shine fim din ta na farko da shine ta fara lashr lambar yabo inda aka bata kyauta jarumar da tafi taka rawar gani a wannan shekarar ta 2019 wato (Best Actress).
Jaruma Hafsat Idris (Barauniya) ta fito a fina finai da yawa sakamakon ca da daraktoci da furodusoshi suka yi mata suka yi ta bata aiki inda kafin kace kobo Hafsat Idris ta zama gabarbadau a Kannywood duk kuwa da tarin jarumai mata da ta tarar a masana'antar, irin su Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Fati Washa, Rahama Sadau, da dai sauran su.
A nan muna yiwa Hafsat Idris fatan alheri da kuma fatan Allah Ya raya mata 'yar jikallen ta alheri da albarka ameen.
*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON).*
No comments