Kumurci yayi sabon aure shekaru 18 bayan rasuwar tsohuwar matarsa Balaraba. *KUMURCI (SHUAIBU LAWAN) YA SAKE YIN WANI AUREN BAYAN RASUWAR ...
Kumurci yayi sabon aure shekaru 18 bayan rasuwar tsohuwar matarsa Balaraba.
*KUMURCI (SHUAIBU LAWAN) YA SAKE YIN WANI AUREN BAYAN RASUWAR MATAR SA BALARABA MUHAMMAD DA SHEKARU 18.*
Jarumi Shu'aibu Lawan Kumurci ya sake yin aure inda ya auri wata budurwa a sirri. Duk da dai wata majiya ta bayyana mana cewa jarumin bai sake yin wani aure ba tun bayan rasuwar matar sa Balaraba Muhammad wadda yaya ce ita ga Maryam Malika ta cikin fim din Malika da kuma Kona Gari shekara 18.
Sai dai majiyar mu mai tushe ta tabbatar mana da cewa bayan mutuwar Balaraba, Shu'aibu Lawan Kumurci ya sake yin wani auren inda ya auri shararriyar mawakiyar fina finai wadda daga bisani ta fara fitowa a cikin fina finai mai suna Maryam Umar Aliyu duk da dai basu dade ba suka rabu inda a karshe ta auri mawaki kuma jarumin fina finai Misbahu M. Ahmad wanda shi yaya ne ga babban darakta Aminu Saira da Naziru Sarkin Waka.
Maryam Umar Aliyu ta fito a cikin fina finai da dama kamar su Dangin Juna, Labarin Zuciya, Makauniyar Yarinya, Khudsiyya, Jani, Sai na Dawo da sauran su.
Kaga kenan wancan lissafin da aka bayar a sama yana da shubuha (tasgaro) kenan domin kuwa Shu'aibu Lawan Kumurci ya auri Balaraba da Maryam Umar sannan kuma ga sabuwar amaryar sa ta sirri wadda ko majiyar mu bata san sunanta ba.
Shu'aibu Lawan Kumurci dai jarumi ne shi a masana'antar Kannywood da ya dade yana jan zaren sa, an dai haifi jarumin ne a Unguwar Gyadi-Gyadi dake cikin birnin Kano, ya kuma shigo harkar fim ne ta dalilin abokin sa Hafizu Bello wanda shima babban mai bada umarni ne a masana'antar ta Kannywood.
Shu'aibu Lawan Kumurci yayi karatunsa na firamare a unguwar Gyadi-Gyadi a wata firamaren unguwar. Ya kuma tafi izuwa makarantar sakandiren KTC Kano, a jihar ta Kano.
Bayan nan Kumurci ya ci gaba da karatu inda ya tafi izuwa Kwalejin Fasaha (College of Technology) inda ya yi karatun koyan zane zane (Art and Design).
Jarumi Shu'aibu Lawan Kumurci ya sami nasarori da yawa tun bayan shigar sa masana'antar ta Kannywood inda yayi fina finai da yawa ya kuma sami lambobin yabo da kuma karramawa daga kungiyoyi, hukumomi da Kamfanoni da dama.
Jarumi Shu'aibu Lawan Kumurci yayi fina finai tare da manyan jaruman na Kannywood irin su Ali Nuhu (Sarki), Sani Danja, Baballe Hayatu, Saima Muhammad, Aminu Sharif Momoh, Abba Al-Mustapha, Saratu Gidado (Daso), Hajara Usman, Nashir Na yaya, Usaini Sule Koki, Tijjani Asase, Sinana, Kazaza, Kabiru Nakwango, Fati Baffa, Maryam Babban Yaro, Safiya Musa, Rukayya Dawayya, Adam M Adam, Sadiq Sani Sadiq, Ibrahim Maishunku, Shehu Hassan Kano, Kabiru Maikaba, Hauwa Katanga, Hafsat Shehu da sauran su.
Kadan daga cikin fina finai jarumi Shu'aibu Lawan Kumurci sun hada da:
Dijangala
Ukuba
Gwamnati
Daba
Ba'asi
Shu'uma
Ruwan Ido
Gadanga
Galaba
Munayat
Farida
Dare Data
Albashi
Zanen Hali
Zaman Idda
Daukaka Da Sira
Albashi
Mazan Fama
Inda Rai
Almustafa
Fansa
Harira
Goma Ta Wuya
Hadarin Habas
Sa'ar Mata
Turare Mai Kamshi da dai sauran su.
A karshe muna yiwa ango (Shu'aibu Lawan Kumurci) fatan alheri Allah Ya bada zaman lafiya da zuriya ta gari.
*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON)*
No comments