Ba Mu Da Alaƙa Da Boko Haram, Cewar Bello Turji Ta’addanci, garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a Arewacin Najeriya musamman yankin Ar...
Ba Mu Da Alaƙa Da Boko Haram, Cewar Bello Turji
Ta’addanci, garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a Arewacin Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma. Jihohin dake fama da matsalar yan bindiga sun hada da Zamfara, Katsina, Sokoto, Kaduna, da Neja.
A jihar Zamfara kadai, an raba mutane akalla 785,000 da muhallansu. Tashar Trust TV ta zanta da kasurgumin jagoran yan bindiga Bello Turji, inda ya bayyana cewa ba shi da alaka da yan Boko Haram.
A cewarsa, su basu da wata akida ko ra’ayiin siyasa. Kawai sun dau makami ne don kare kawunansu. A cewarsa: “Bamu da ra’ayin kafa wata kungiyar addini. Bamu da niyyar yanke wata kasa, kuma babu ruwanmu da siyasa.
Mun dau makami ne don kare rayukan al’ummarmu da ake kashewa.” “Ba wai bamu da imani bane ko bamu da tsoron Allah ba.” Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, ni makiyayi ne.
Bello Turji Turji, wanda dan asalin garin Fakai a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa wadanda suka san shi sun yi mamakin yadda ya fara sata da kashe-kashe.
Turji ya kara da cewa a rana guda aka kashe masa yan uwa shida bayan sacewa iyayensa Shanu sama da dubu. Haka yasa ya dau bindiga don kare hakkin Fulani yan uwansa da aka takurawa a karamar hukumar Shinkafi ta jihar.
No comments