Shugaban Ukraine ya caccaki shugabannin kungiyar tsaro ta NATO saboda ƙin aiwatar da hana shawagin jirage a ƙasarsa. A cikin wani kakkausan...
Shugaban Ukraine ya caccaki shugabannin kungiyar tsaro ta NATO saboda ƙin aiwatar da hana shawagin jirage a ƙasarsa.
A cikin wani kakkausan jawabi, Volodymyr Zelensky ya ce jan ƙafar da ƙasashen yammaci ke yi na shiga tsakani ya ba Rasha “ƙarfin guiwa” na ci gaba da kai hare-hare a garuruwa da kauyukan Ukraine.
Nato ta ce matakin hana shawagin zai haifar da fito na fito da Rasha.
A ranar Asabar ɗin nan shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya yi gargaɗin cewa ɗaukar mataki irin haka zai kasance a matsayin “amincewa da shiga yaƙi ne da ƙasar ta yi.”
Dangane da takunkumin da kasashen Yamma suka kakaba wa Rasha, shugaban na Rasha ya ce “matakin ya yi kama da tallar yaƙi, amma sai godiyar Allah hakan ba ta faru ba.
A cikin jawabinsa daga Kyiv, Mista Zelensky ya ce bai amince da cewa ɗaukar matakin kai tsaye zai iya haifar da wuce gona da iri kan kungiyar tsaro ta Nato ba. A cikin fushi kuma ya bayyana cewa “ra’ayin ƙasashen yammaci ya nuna cewa ba su ɗauki gwagwarmayar neman ƴanci ba a matsayin burin farko na ƙungiyarsu ba.
"Mutanen za su mutu tun daga wannan rana saboda ku, saboda rauninku, saboda rashin hadin kan ku," in ji Mista Zelensky.
-BBC
No comments