Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Da Dumi Dumi: wata mata ta kama barawo da karfin tuwo a Zariya

  Da Dumi Dumi: wata mata ta kama barawo da karfin tuwo a Zariya  Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel "Wata mata mai suna magajiya hai...

 Da Dumi Dumi: wata mata ta kama barawo da karfin tuwo a Zariya 


Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel

"Wata mata mai suna magajiya haifaffen garin zariya, ta yi nasarar kama barawo da karfin tuwo a yayin  da ya shigo dakinta a domin sace mata kamfuta bayan ta saka a caji a cikin Daren ranar sabat din da ta gabata." 

"Labarin na cewa, matar ta fito daga daki Sai ta tafi ban daki ta bar kofar dakinta bude sauran yara suna barci." 

Jim Sai ga barawon ya shigo cikin gidan bai tsaya a ko'inaba Sai a dakin wannan matar, da shigar barawon ba wuya! Sai ya rumfaci sabuwar kamfuta dal ansaka a caji."

Bayan barawon ya saci kanfutan yazo fitowa daga dakin, Ashe malama magajiya tamake daga gefen kofa ta waje hannunta dauke da wani shirgegen muciya, nan magajiya ta rangada ma wannan barawon muciya ga bisa Kansa, barawo nan dai ya yi warwas zuwa kasa bai San inda yake ba tare da kamfutan."

Daga bisani malama magiya ta saka ihun barawo aka zo aka kama shi, kana magajiya ta dauki kamfutarta ta koma da shi cikin daki

"Inda rahoto ke tabbatar mana cewa, kamfutar ta samu matsalar fashewar glishi wato "Screen" amma cikin ikon Allah kamfutar ta kawo kamar yadda take."

"Wannan al'amarin ya farune a wani unguwa da ake kira da mazangudu, gidan sha'aban mai doya cikin birnin zariya."

No comments